Ndume ya ƙi amincewa da shugabancin kwamitin majalisa, ya ce yana kan kalamansa

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Daga ƙarshe, Sanata Ali Ndume ya yi jawabi kan cire shi a matsayin Mai Tsawatarwa a majalisar dattijai inda ya ce bayan yin nazari kan abin da ya sa aka gaggauta sauke shi, an kuma fahimci hakan bai bada damar korar sa ba.

Majalisa ta tuɓe Ndume daga muƙaminsa ne bayan da ya caccaki tsarin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu kan yadda ya ke tafiyar da harkokin gwamnati.

Haka kuma, bayan kwana biyu da faruwar haka ne Ndume ya ƙi karɓar muƙamin shugaban kwamitin walwala na majalisar inda ya ce bashi da kwarewa da muradin shugabantar ɓangare mai buƙatar kula kamar wannan.

Ndume wanda ke wakiltar Borno ta Kudu, ya faɗi hakan ne bayan sauke shi daga muƙamin Mai Tsawatarwa, a gidansa da ke Maiduguri inda ya ce bai taɓa cewa yana buƙatar matsayin Mai Tsawatarwa ba.

Yayin da yake magana game da batun sauya sheƙa zuwa wata jam’iyya, Ndume ya bayyana cewa, kasancewarsa ɗaya daga cikin jagororin kafa jam’iyyar APC, kuma wanda ya bada gudunmawa ga kafa shugabancin Godswill Akpabio, sai ya yi shawara da mutanensa.

By Babaji