
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Hukumar almajirai da ilimin yaran da ba sa zuwa makaranta (NCAOOSCE) tare da haɗin gwiwar kwamishinonin ilimin a wasu jihohin Arewa sun ƙudiri aniyar shiga lungu da saƙon ƙananan hukumomi shida na Abuja don zaƙulo yara 10,000 da ba sa zuwa makaranta domin sanya su a makarantu kafin watan Satumba.
Sakataren hukumar, Mohammed Idris ya faɗi haka a ranar Juma’a, yayin gudanar da taron ƙaddamar da aikin zaƙulo yaran a babban ofishinta da ke Abuja.
Idris, ya yaba wa shugaba Bola Tinubu kan goyon baya da ya ke basu a ƙoƙarinsa na magance matsalolin almajiranci da yaran da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya.
Ya ƙara da cewa, hukumar tana cigaba da ƙoƙari wajen tabbatar da babu yara da ke gararamba, ko maraice da ma rashin zuwa makaranta a cikin al’umma nan ba da jimawa ba.
A watan Mayu, Ministan ilimi, Tahir Mamman ya bayyana cewa, haɗe karatun zamani da tsarin almajiranci shi ne mafita ga yaran da ba sa zuwa makaranta a Arewa inda ya ce ma’aikatar ta saka yara sama da miliyan biyu a makaranta ta hannayen hukumomi da dama.
