Gwamnatin Tarayya na shirin ɗora wa bankuna harajin 50% a kan ribar da suka samu wajen hada-hadar kuɗin ƙasashen waje da suke yi. Wannan yunƙurin za a yi shi ne domin tallafawa wa gwamnatin ganin ta iya biyan ƙarin albashi da ta sanar. Wannan bayanin na zuwa ne, daga shafin Imran Muhd wanda ɗan jam’iyyar APC ne.
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya aika wa majalisa kwaskwarima a kan dokar kuɗi domin samun amincewar su. Wannan ƙudurin yana cikin hanyoyi da gwamnatin za ta bi domin magance matsalolin tattalin arziki.
Sabon harajin ana sa ran zai ƙara ma gwamnati kuɗin shiga, zai samar da isassun kuɗaɗe domin aiwatar da sabon tsarin albashi. Wannan ƙudurin ya cigaba da nuni da yadda gwamnati ke ƙokari wajen ganin an samu daidaito a lamarin kasafin kuɗi gaba ɗaya ƙasar.
