Daga RABI’U SANUSI a Kano
An jaddada yunƙurin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ƙoƙarin kawo canjin bai ɗaya a ɓangaren noma a faɗin Jihar Kano baki ɗaya.
Wannan na zuwa ne daga bakin shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Gwale Hon Abubakar Mu’azu Moja a wata zantawa da manema labarai yayin da tawagar sa suke adana takin da aka basu tare da sauran Kansilolin sa baki ɗaya.
Hon Abubakar Mojo ya ce, a yadda mai girma Gwamna Abba Kabir ya mayar da hankali wajen canza akalar jihar ta hanyoyi daban-daban domin ci gaban jama’ar sa.
Hon Mojo ya kuma bayyana cewa shima a ƙaramar hukumar Gwale yayi shi mai girman gaske na kawo canji na cigaba da za su tallafawa jama’ar sa.
“Sakamakon buƙatar taimakon ƙaramar hukumar Gwale ya sa muka tashi tsaye tare da fita domin samo hanyoyin da za su bamu damar tallafama mutanen mu domin ba su damar tsayawa da ƙafafun su baki ɗaya.”
Kantoman riƙon ya jaddada cewa ya zuwa yanzu dai sun yi shiri na musamman don ganin yadda mai girma Gwamna ya ba su wannan amana sun isar da ita yadda yakamata.
“Yadda kuke gani yanzu haka akwai wannan taki da gwamnati ta amince mana mu raba ga al’umma asalin manoman ƙaramar hukumar Gwale don haka za mu bada kamar yadda aka umarce mu.”
Abubakar Mojo ya tabbatar ma da al’ummar wannan jiha cewa shi dai ya daɗe bai ga an bada takin noma ga manoma kai tsaye daga tushe ba tun lokacin jagora Dr Rabiu Musa Kwankwaso sai a wannan karo na magajin sa.
“Bayan wannan dama da aka bada na tallafin taki, haka zalika akwai batun ayyukan da za mu gabatar irin na gyaran magudanan ruwa da samar ma matasa hanyoyin dogaro da kai.
Kantoman ya kuma buƙaci jama’ar jihar da su ƙara dagewa wajen ci gaba da yima Gwamna Abba Kabir addu’a da jihar baki ɗaya.
