NFF ta fara horar da mata aikin koci a Nijeriya

Spread the love

Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya, Ibrahim Gusau, ya ce nan da ƙarshen shekarar nan, hukumar za ta shirya taron bita ga masu horar da ’yan wasa maza a ƙasar.

Wannan dai na zuwa ne bayan da aka shirya makamanciyar bitar ga masu hararwa mata, da aka fara a ranar Litinin.

A cewar Gusau, horon da aka faro a jiya somin-taɓi ne, domin ana sa ran kafin ƙarewar wannan shekarar za a gudanar da makamantansa na ɓangaren masu horarwa maza har karo biyu.

Ka san kuma wannan shi ne karo na farko da aka taɓa shirya wa masu horaswa mata, har ma a yayin buɗe wa a jiya shugaban hukumar ya yi alƙawarin ci gaba da ƙarfafawa Masu horarwa Mata gwiwa.

Nasiru, ka san tun a shekarar 2017 ne, rabon hukumar ta NFF da ta shirya makamancin wannan horo, wanda a lokacin kusan masu horas da ’yan wasa 80 daga sassan ƙasar ne suka hallaci taaron bitar da ya gudana a Abuja babban birnin ƙasar, ka san kuma bayan kammala wa akan bai wa koci-kocin lasisin horarwa.

A cewar daraktan tsare-tsare na hukumar ta NFF, Augustine Eguavoen, ya ce wannan horon bitar na masu horasawa mata ya ƙunshi nau’o’i uku ne, inda za a fara gudanar da darusa kashin farko daga ranar 15 zuwa 25 ga watan da mu ke ciki na Yuli, sannan za a gudanar da horo na tsawon mako biyu ga koci-koci tsakanin ranar 27 ga watan na Yuli zuwa 7 ga watan Agusta mai kamawa.

Eguavoen ya kuma ce za su sake komawa Abuja a karo na biyu domin gudanar da darusa daga ranar 12 zuwa 20 ga watan Agusta, daga nan kuma za su ƙara karɓar horo na tsawon mako biyu daga ranar 23 ga Agusta zuwa 3 ga Satumba.

Sai nau’i na uku wanda a shi ne za a gudanar da jarrabawa, shi kuma zai fara ne daga 9 zuwa 19 ga watan Satumbar wannan shekara.

Ya ce daga cikin waɗanda za su bayar da horon akwai Terry Eguaoje da Ladan Bosso da Wemimo Olanrewaju da kuma Lanrence Ndaks.

By ukarofi