Ɗan wasan gaba na gefe na Leeds Crysencio Summerɓille, mai shekara 22, ya tattauna da Chelsea, to amma kuma ƙungiyar Rennes ta Faransa, ita ma ta yi magana da ɗan Holland ɗin.
Huddersfield Town na tattaunawa domin sayen ɗan wasan tsakiya na Wolɓes Joe Hodge, mai shekara 21, bayan da ɗan wasan na tawagar Jamhuriyar Ireland ta ‘yan ƙasa da shekara 21 ya shafe kakar da ta wuce a zaman aro a Ƙueens Park Rangers.
Barcelona ta gabatar da buƙatarta ga ɗan wasan gaba na gefe na Athletic Bilbao Nico Williams, mai shekara 22, a ƙoƙarin cimma yarjejeniya ta baki da ɗan Sifaniyan kafin wata ƙungiya ta Ingila ta neme shi.
West Ham ta yi nisa a tattaunawar sayen ɗan bayan Manchester United. Aaron Wan-Bissaka, mai shekara 26.
Matashin ɗan wasan tsakiya na Eɓerton Amadou Onana na Belgium, mai shekara 22 na daf da kammala komawarsa Aston Villa zuwa ƙarshen makon nan.
Tsohon kocin Liverpool Jurgen Klopp ba shi da sha’awar karɓar aikin horar da tawagar Ingila.
A shirye hukumar ƙwallon ƙafa ta Ingila take ta jira Pep Guardiola ya bar Manchester City kafin ta naɗa shi a matsayin wanda zai maye gurbin Gareth Southgate a matsayin koci na dindindin.
Shi ma kocin Tottenham Ange Postecoglou na daga cikin waɗanda ake sa ran zaɓa domin maye gurbin na Southgate.
Fafutukar Al Nassr ta neman mai tsaron ragar Juventus Wojciech Szczesny na Poland, mai shekara 34 ta gamu da tazgaro.
Paris St-Germain ta ƙara dagewa a ƙoƙarin da take na ganin ta sayi ɗan gaban Napoli, Ɓictor Osimhen na Nijeriya, abin da zai iya kawo ƙarshen zawarcin ɗan Nijeriyar da Chelsea ke yi.
Kusan Liverpool ta janye daga fafutukar sayen ɗan bayan Lille, wanda zai tafi Manchester United Leny Yoro, mai shekara 18, saboda alamu sun nuna yana sha’awar tafiya Real Madrid ne kawai.
Ƙungiyar Birmingham City na sha’awar matashin ɗan gaban Aston Villa Louie Barry, na Ingila.
Har yanzu kuma Bayer Leɓerkusen na bin Villa sama da rabin kuɗin cinikin ɗan wasan gaba na gefe Moussa Diaby, na Faransa mai shekara 25, wanda ya kusa tafiya Al Ittihad ta Saudiyya.
West Ham na samun nasara a ƙoƙarin sayen ɗan gaban Arsenal Reiss Nelson, mai shekara 24, ɗan Ingila da Gunners ta yi wa kuɗi fam miliyan 25.
Aston villa na shirin gogayya da Chelsea da Barcelona a kan sayen ɗan wasan gaba na gefe na Athletic Bilbao Nico Williams, mai shekara 22, wanda ya yi wa Sifaniya wasa a gasar cin kofin ƙasashen Turai da aka kammala, Euro 2024.
Al-Nassr ta kawo ƙarshen cinikin mai tsaron ragar Manchester City Ederson, mai shekara 30, bayan da Cityn ta ƙi tayinta na yuro miliyan 30, abin da ya sa ƙungiyar ta Saudiyya yanzu ta karkata ga cinikin takwaransa na Brazil Bento, wanda ke wasa a Athletico Paranaense.
Arsenal na sa ran samun ƙarin tayi a kan ɗan wasanta na tsakiya Emile Smith Rowe bayan da ta ƙi yarda da tayin Fulham, inda yanzu Crystal Palace ma ke son ɗan wasan ɗan Ingila.
Cole Palmer ya yi ƙoƙarin shawo kan abokin wasansa na Ingila, kuma ɗan gaban Aston Ɓilla Ollie Watkins, mai shekara 28, a kan ya koma Chelsea a bazaran nan.
Leicester City ta gabatar da tayin fam miliyan 21 da ƙarin wasu tsarabe-tsarabe na fam miliyan 4 a kan ɗan wasan tsakiya na Argentina Matias Soule, mai shekara 21, to amma kuma ƙungiyarsa Juventus, da ke son aƙalla fam miliyan 25 da ta ƙi sallamawa.
