Daga ABDULLAHI SANI MUSA a Kano
An bayyana tallafa wa ɓangaren noma shi zai samar da wadataccen abinci a Nijeriya, matuƙar gwamnati za ta tallafa wa ƙanana da manyan manoma a ƙasar.
Wani masani kan dabarun noman zamani daga Jihar Jigawa, kuma shugaban sashin lura da lamuran yau da kullum a babban gidan gonar A.I.G Ringim, Alh. Yakubu Moh’d Tsagan, shine ya furta hakan yayin ganawarsa da ‘yan jarida a farfajiyar gidan gonar A.I.G.
“A don haka kama ta ya yi masu ruwa da tsaki kan dabarun noma irin na zamani a gwamnatance da su taimaka su bai wa gwamnatin taryya shawarwarin da suka dace wajen samar da tallafin kayan noma na zamani, ga ƙananan manoman yankun karkara da suka haɗar da samar da takin zamani, irin shuka da dai sauransu.”
Tsagan kamar ya nuna damuwarsa kan yadda tallafin noma da gwamnati kan bayarwa domin raba shi ga talakawan ƙasar nan na karkara ke tsayawa a hannun wasu shafaffu da mai, da cewa yin hakan ba ƙaramin naƙasu ba ne.
A fannin harkar noma a Nijeriya, inda ya ba da misali da gidan gonar tsohon A.I.G na Kano, wato Ringim, cewa mutane ne da dama ke cin arzikin gidan a ɓangarori daban-daban, a wani mataki na ragewa gwamnati yawan matasa marasa ayyukan yi. Alh. Yakubu Tsagan daga bisani sai ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga masu ruwa da tsaki kan bayar da tallafin da su rinƙa bibiyar tallafin kayan noman da nufin tabbatuwarsa ga hannun waɗanda ya dace ya je gare su
