Daga DAUDA USMAN a Legas
Wani basarake a Jihar Ogun kuma fitaccen ɗan kasuwa a garin Ogere, Alhaji Kabiru Mustapha, wanda shi ne Magajin Garin Hausawan Ikwairu a Jihar Ogun, ya shawarci maniyatan Nijeriya da za su je ƙasa mai tsarki domin gudanar da aikin Hajjin bana da su kasance masu tsoron Allah tare da kiyaye dokokin ƙasar Saudiyya.
Alhaji Kabiru Mustapha, wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar masu sana’ar kasuwancin karahuna (bola jari) tare da kasancewa mai ba da shawara na musamman a fadar Mai Martaba Sarkin Yarbawan Ikwairu, ya bayar da wannan shawara ne yayin da yake yi wa wasu maniyata daga yankunan Ikwairu da Ogere bankwana kafin tafiyarsu zuwa ƙasa mai tsarki.
Ya ce ya zama wajibi maniyata su ƙara himma wajen sanya tsoron Allah a zukatansu tun daga lokacin da suka fara tafiya zuwa Saudiyya har zuwa lokacin da za su kammala ibadunsu.
Magajin Garin Hausawan Ikwairu ya kuma buƙaci maniyatan su zama jakadu nagari na Nijeriya a ƙasa mai tsarki ta hanyar nuna ɗabi’u nagari da kiyaye mutuncin ƙasarsu.
Ya gargaɗi maniyatan da su nisanci duk wani nau’in haramtacciyar sana’a, musamman safarar miyagun ƙwayoyi da sauran kayayyakin da doka ta haramta, yana mai cewa irin waɗannan ayyuka suna jefa mutum cikin matsala tare da bata sunan Nijeriya.
A cewarsa, ya kamata maniyyaci ya mai da hankali kan ibadar da ta kai shi ƙasa mai tsarki maimakon shiga harkokin da za su iya jawo masa matsala ko rage masa lada.
“Mutumin da ya tafi aikin Hajji ya tafi ne domin neman gafarar Allah da tsarkake rayuwarsa. Bai kamata ya ƙara wa kansa wani sabon nauyi ta hanyar aikata abubuwan da suka saɓa wa doka da koyarwar addini ba,” inji shi.
Ya kuma yi addu’ar Allah Ya bai wa maniyatan Nijeriya aikin Hajji karɓaɓɓe, tare da fatan za su dawo gida lafiya bayan kammala ibadunsu.
A wani ɓangare na jawabinsa, Alhaji Kabiru Mustapha ya nuna damuwarsa kan abin da ya bayyana a matsayin takurawar da wasu jami’an gwamnati a Jihar Ogun ke yi wa masu sana’ar karahuna.
Ya ce jami’an na yawan zuwa wuraren da suke tara kayayyakinsu suna neman takardun shaidar saye (rasit), lamarin da ya ce yana kawo cikas ga harkokin kasuwancinsu.
A cewarsa, kayan karahuna abubuwa ne da aka riga aka yi amfani da su kuma aka zubar da su, waɗanda masu sana’ar ke tattarawa domin sayarwa ga kamfanonin da ke sake sarrafa su.
Ya yi kira ga gwamnatin Jihar Ogun da ta dubi halin da masu wannan sana’a ke ciki tare da samar da mafita domin sauƙaƙa musu gudanar da kasuwancinsu cikin lumana da bin doka.
