Wani da ake zargin ɗan fasa ƙwauri ne ya kashe jami’in kwastom a Kaduna

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Kwastom ta Nijeriya, sashin ayyuka na tarayya, Shiyya ta B, ta sanar da rasuwar wani Insifekta na Kwastom, IC, Hamza Abdullahi-Elenwo.

Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a a yayin da ake gudanar da aikin bincike a Achilafia daura da hanyar Daura zuwa Kano a Jigawa.

Bayanin hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na sashin ayyuka na tarayya shiyyar B Kaduna, SP Isah Sulaiman ya fitar.

A cewarsa, an tsare wanda ake zargin yayin da Kwanturola Ahmadu Shuaibu ya sha alwashin tabbatar da adalci ga jami’in da aka kashe.

Mista Sulaiman ya ce, “Lamarin ya faru ne a lokacin da wata mota da ake zargin an shigo da ita ƙasar nan ta ɓarauniyar hanya, ta afka wa jami’in da ke ƙoƙarin gujewa kama shi.

“An garzaya da marigayin zuwa Babban Asibitin Kazaure, daga bisani kuma aka kai shi Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) Katsina, inda Likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da rasuwarsa.”

An haifi Insifekta Hamza, ɗan asalin garin Fatakwal, Ribas, a ranar 15 ga Afrilu, 1985.

“Ya shiga Hukumar Kwastom ta Nijeriya a matsayin Mataimakin Shugaban Kwastaom III (CAIII) a sashin sufuri da dabaru a ranar 17 ga Oktoba, 2013, kuma an ƙara masa girma zuwa muƙamin Sufeto na Kwastom (IC) a shekarar 2022.

“Ya rasu ya bar matarsa ​​da ‘ya’yansa biyu, kuma an binne gawarsa a Katsina kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

“Shuaibu, a madadin ɗaukacin hafsoshi da jami’an rundunar, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin tare da yi masa addu’ar Allah ya huta.

“Shuaibu ya lura cewa lamarin ya nuna irin halin da ake ciki a tsakanin masu fasa-ƙwaurin da suke gudanar da ayyukansu ba tare da kula da rayuwar bil’adama ba,” Mista Sulaiman ya kara da cewa.

Ya ƙara da cewa wannan na ɗaya daga cikin lokuta da dama da ‘yan fasa ƙwabrin suka kashe tare da raunata ma’aikatan hukumar a ƙoƙarin gujewa kama su.

Kakakin ya ruwaito Shu’aibu ya sha alwashin tabbatar da cewa an yi adalci, ya ƙara da cewa, “An kama wani mutum da ake zargi yana hannun rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Gwiwa da ke Jigawa.

“Jami’an sashin ba za su yi kasa a gwiwa ba kuma za su ci gaba da kasancewa a cikin yƙi da fasa ƙwauri.”

By ukarofi