Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Bankin Afirka, AfDB, Akinwumi Adesina ya gargaɗi gwamnatin tarayya cewa shirin ta na bada damar shigo da kayan abinci ƙasar ka iya lalata ɓangaren noma.
Adesina ya yi gargaɗin ne a wani taro a Abuja da cocin anglican ta shirya.
Ya ƙalubakanci gwamnatin Nijeriya da gwara ta samar da isasshen kayan abinci tare da samar da ayyukan yi a fannin noma.
A tuna cewa a ranar 10 ga watan Yuli ne Ministan Harkokin Noma, Abubakar Kyari ya sanar da dakatar da haraji ga kayayyakin abinci da za a riƙa shigo da su ta bodojin ƙasar har tsawon watanni biyar.
A gefe guda kuma, matasa da wasu ƙungiyoyi a Nijeriya sun ɗaura ɗambar shirya zanga-zanga a faɗin ƙasar a ƙarshen watan nan, domin nuna takaici kan tsadar kayan masarufi da ke ƙara ta’azzara a Nijeriya. Sai dai ana cigaba da samun bambance-bambance ra’ayi akan zanga-zangar, inda har wasu malamai ke nuna haramcin yinta a addinin Musulunci, wasu kuma suna ƙarfafa wa matasa.
