Yadda aka kama wasu ‘yan luwaɗi a Gombe

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar ’yan sandan jihar Gombe ta kama matasa biyu da ake zargi da aikata luwaɗi.

Da yake gabatar da waɗanda ake zargin a hedikwatar rundunar, ASP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa, a ranar 11 ga watan Yulin 2024, rundunar ta samu labarin cewa an kama waɗanda ake zargin suna saduwa da juna ta dubura a unguwar Kanbariki da ke garin Kumo.

Daga nan rundunar ta je wuri ta cafke waɗanda ake zargin inda aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

Buhari ya bayyana cewa a lokacin da ake gudanar da bincike waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu.

Ya ce ɗaya daga cikinsu ya bayyana cewa ɗayan ya yi alƙawarin ba shi kuɗi N15,000 idan suka kammala.

Amma bayan ya samu biyan buƙatar tasa sai ya nuna masa cewa ba zai ba shi kuɗin ba.

Jami’in ya ce nan ba da jimawa ba za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

By ukarofi