Na sha wahala sosai wajen aikin fim ɗin ‘Wata Tafiya’ – Alfazazee

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Alfazazee Mohammad fitaccen daraktan da ya yi suna a masana’antar shiryar finafinai ta Kannywood, wanda kuma ya bada umarni a manya-manyan finafinan da duniyar Kannywood ta ke alfahari da su, kuma wanda ya bada umarni a finafinan manyan jarumai maza da mata. A wannan makon, Manhaja ta samu damar tattaunawa da shi domin jin ta bakin sa musamman a ɓangaren sa na bada umarni da wasu batutuwan daban:

MANHAJA: Za mu so jin taƙaitaccen tarihinka da kuma sana’arka.

ALFAZAZEE: To ni dai sunana Alfazazee Mohammad, an haife ni a cikin garin Kaduna, a nan na girma kuma na yi karatu duk a cikin garin Kaduna. Ina da mata da ‘ya’ya guda biyu. Na fara harkar fim tun wajen shekarar 2000.

Me ya sa ka ɗauki ɓangaren bada umarni a cikin sana’ar?

Da farko na fara da ɓangaren rubutun labari ne, wato ‘Script Writing’ da kuma fita a matsayin jarumi, inda na rubuta wani labarin fim mai suna ‘Ƙuruciya’. Sannan na fito a matsayin jarumin shirin wanda Alhassan Kwalle ne ya bada umarni. Daga nan sai kuma na ji ba na sha’awar fita a cikin fim kuma, shi ne na koma rubutu da kuma bada umarni. Amma kuma duk sha’awa ce ta kaini ga hakan.

Kana da ubangida ne da ya fara nuna maka yadda ake bada umarni ko kuwa kawai ka tsinci kanka ne a ciki?

To gaskiya dai da farko na fara harkar ba ni da wanda ya koya min sai abin da na fahimta a wajen kallon finafinai da kuma aiki da na ɗan yi da wasu daraktoci. Daga baya sai Allah ya haɗa ni da Ali Nuhu wanda na fara yi masa mataimakin mai bada umarni. To haɗuwa ta da shi ne na koyi abubuwa da dama a ɓangaren bada umarni.

Zuwa yanzu finafinai aƙalla guda nawa ne ka bada umarni a cikinsu?

Gaskiya ba zan iya tuna yawan finafinan da na bada umarni ba domin su na da matuƙar yawa.

Wane fim ka fi so a cikin waɗanda ka bada umarni?

Gaskiya duk fim ɗin da na yi ina son su kuma ina alfahari da su sosai.

Wane ya fi ba ka wahalar aiki kuma?

Fim ɗin ‘Wata Tafiya’ shi ne fim ɗin da ya ba ni wahala saboda ‘action’ ne, shi ne ‘action’ da na fara bada umarni.

Wanda ka fi jin daɗin aikin sa fa?

(Dariya) Aiki ai ba daɗi gaskiya.

Wane ƙalubale ka taɓa fuskanta ko ka ke fuskanta ɓangaren bada umarni?

Ƙalubale bai wuce na haɗuwa da jarumai da ba su da fahimta ba, ma’ana ba su iya ‘acting’ ba. Idan an ce su yi abu kaza sai su kasa yin shi, ko da kuwa za ka kwana ka na nuna masu, sai dai su yi shi yadda su ka iya amma ba yadda ka ke so ba. Saboda haka gaskiya ina shan wahala wajen koya musu abin da za su yi.

Kusan duk finafinan Ali Nuhu kai ka ke bada umarni. Menene sirrin hakan?

Ali Nuhu maigidana ne kamar yadda na faɗa a baya, a wajen sa na san abubuwa da dama, kuma wajen sa na koyi bada umarni; shi mutum ne wanda ba shi da mugunta ko ƙyashin nuna maka wani abu, saboda haka na bada umarni sosai a finafinansa wasu kuma na yi masa mataimakin mai bada umarni.

A lokacin da ka ke marubucin fim ka taɓa rubuta labari na zube?

Ban taɓa rubutun zube ba duk da ina da sha’awar hakan a raina.

Wani lokacin za ka samu masu harkar fim ba a harkar fim kawai su ka tsaya ba, sukan yi wasu abubuwan a wajen masana’antar kamar sana’a haka. Shin ko ka na cikinsu?

Gaskiya ba na samun lokacin aiwatar da wani abun daban, saboda rashin lokaci, kodayaushe ina kan aiki.

Wasu na ɗora laifin abubuwan da wasu daga cikin taurarin Kannywood ke yi a kan manyan shugabannin ta, ana ganin su ne ba sa yi wa tufkar hanci. Me za ka ce game da wannan?

Shi laifi dama an ce ai tudu ne, bai kamata ma a ɗora laifin wani a kan wani ba, yin hakan ba adalci ba ne. Idan babba ya yi laifi to a ba shi laifin sa, idan ƙarami ya yi laifi to a bar shi da laifin sa.

Wane kira za ka yi ga marubutan fim?

Ina kira ga marubutan fim da a dinga natsuwa wajen yin rubutu a daina sauri, su daina biye wa ‘Producers’, wato masu zuba kuɗaɗensu su shirya fim, a tsaya a yi rubutu da kyau kuma mai ma’ana, saboda labari shi ne ƙashin bayan fim.

Shin akwai wani shiri da ake yi kan magance matsalar fitar finafinai marasa ma’ana?

Tabbas akwai shiri da ake yi na ganin an kawo gagarumin sauyi wajen yin finafinai masu ma’ana da za su ilimantar da al’ummarmu.

Mun gode ƙwarai.

Ni ma na gode.

By ukarofi