Wahalar man fetur: ’Yan Nijeriya na cikin tasku!

Spread the love

Assalamu alaikum, Edita, da fatan kana lafiya. Allah ya albarkaci jaridar Blueprint Manhaja.

Ƙarancin Man Fetur a sassan ƙasar nan ya ƙara ci gaba, yayin da ’yan Nijeriya ke sayen litar mai tsakanin N750 zuwa N850.

Lamarin ya fi muni ga mazauna Kaduna, Abuja da kuma Legas, cibiyar kasuwancin Nijeriya.

Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya ta ce, a makon da ya gabata ta gano wani mai da aka gauraya da methanol, kuma ta janye man daga sassan Nijeriya.

A cewar wani mai sarrafa man, an keɓe ƙayyadaddun adadin samfurin man da abin ya shafa kuma an cire shi daga kasuwa, gami da manyan motoci masu dako.

Sakamakon haka, Shugaba Bola Tinubu ya umurci hukumomin da suka dace da su sanya takunkumi ga duk waɗanda ke da hannu wajen shigo da wannan gurɓatattun mai.

Ko da yake an samu tabbacin kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPC) na cewa lamarin zai lafa, amma babu wani abu da ke nuna hakan zai kawo ƙarshen abin nan ba da daɗewa ba.

Wannan matsala ta sa wasu matafiya, musamman ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu sun maƙale, inda wasu ke biyan maƙudan kuɗaɗe sama da kashi 100 na zirga-zirgar zuwa inda suke.

Yayin da ’yan baƙar kasuwar suka jeru manyan tituna suna sayar da mai da tsada ba tare da damuwa ba, direbobin motocin ’yan kasuwa su ma sun ƙara kuɗin abin hawansu.

A kan titin filin tashi da saukar jiragen sama na Lugbe, wasu matasa suna sayar da galan ɗin man fetur mai lita 10 akan farashi mai tsada daga N7,000 zuwa N10,000.

Ya kamata gwamnati ta sake zage damtse wajen ganin an kawo ƙarshen wannan mummunar wahala ta ƙarancin da tsadar man fetur.

Allah ya sa mu dace, Ameen

Saƙo daga Malam Sa’id, 09070905293.

By ukarofi