Daga ALI ABUBAKAR SADIƘ
Malamai magada annabawa, ita ce mafi girman martaba da ake alaƙanta malamai da ita, domin a tsarin Musulunci malamai su ne garkuwar ɗabbaƙa “Amru bil Ma’aruf da Nahyi anil Munkar”, darajar da ta sa Allah da kansa ya ce mana mu Musulmi “Kuntum khaira ummatin” (mafi alherin mutane).
Wannan dalilin ya sa a arewacin Najeriya mu ke biyayya sau da ƙafa ga malamanmu na addini. Amma a ɗan tsukukun nan jama’a sun sami ruɗani, saboda kasancewar wasu daga cikin malaman, koda yake su ne ƙalilan, na bayar da fatawar cewa zanga-zanga halal ce, amma akasari sun karkata ga cewa babu zanga-zanga ga mahukunta a Musulunci.
Cikin ƙalilan da suka yarda cewa jama’a na iya zanga-zanga akwai Sheikh Ahmad Gumi, kamar yadda ya faɗa a wata hirar BBC, sannan da fitattun malamai biyu da su ka riga mu gidan gaskiya; Sheik Albani Zaria da Sheikh Jafar Mahmud Adam.
Tambayoyin da matasan Arewa ke nema a wannan gaɓa daga malaman Arewa da ke ce musu kada su fito zanga-zanga, domin fayyace musu sahihanci ko akasin haka sune:
1. Akwai wata aya guda ɗaya da ta ce ƙarara kada Musulmi ya nuna fushinsa akan mahukunta idan sun zalunce su?
2. Idan akwai wannan ayar, to mene ne matsayinta da ayar cikin Suratul Nisa’i (Q4:148) da ta ce, “Allah bã Ya son bayyanãwa da mũnãna daga magana, FÀCE ga wanda aka zãlunta.” Shin zanga-zanga ba nuna fushin wanda aka zalunta ba ne?
3. Akwai wani hadisi da ya ce kada Musulmi ya nuna ƙorafinsa ga mahukunta idan ya na zargin zaluncin?
4. Idan akwai hadisin, to mene ne matsayinsa da hadisin da Umar yana kan mimbari wani ya ƙalubalance shi da yin bayanin yadda ya sami gyauto biyu maimakon ɗaya da aka bai wa kowa daga ganima? Nan take ya ce, ɗansa, Ibn Umar, ya yi bayani. Ko kuma uwa-uba ma, yadda wasu Ansarai su ka yi ƙorafin Annabi (SAW) ya yi son kai wajen raba ganimar Hunayn, amma Annabi (SAW) ya tsaya ya yi bayanin gamsar da su?
5. Shin a lokacin Jonathan su wane ne su ka fito su ka yi ta tsine masa a mumbarin Juma’a da tunzura mutane? A lokacin me ya sa ba su fito sun hana ’yan Arewa zanga-zanga ba? Ko a lokacin ba haram ba ce a wajensu?
6. Mene ne hukuncin wanda ya haɗa kai da azzalumi ko ya bai wa azzalumi kariya? Musulunci ya yarda da kare zalunci?
7. Shin shugaba a tsarin Musulunci daidai yake da shugaba a tsarin dimukraɗiyya? Ana iya daidaita biyayya ga biyun?
8. Shin Musulunci ya halasta dimukraɗiyya? Idan ya halasta ta, to zanga-zanga tsari ce cikin dimukraɗiyya, sai dai idan kuma sun haramta dimukraɗiyyar?
9. Me ya sa malamai ke mara wa ’yan siyasa bayan sun karɓo tallansu sannan su yi musu kamfen?
10. Me ya sa malaman Arewa su ka ɗauko tallan Muslim-Muslim da sunan addini, amma gwamnati ta gaza ƙarara, amma kuma ana amfani da addini a hana a yi ƙorafi?
11. Me ya sa malamai ba wanda ya ce uffan da aka cire tallafin mai wanda ya jefa ƙasa a bala’in da ba a taɓa shiga ba? Amma su ka yo caa kan talaka don kada ya yi ƙorafi?
12. Me ya sa ba za ka taɓa jin malamai na tayar da jijiyar wuya, saboda talakawa da ake kashewa ba, duk da sanin cewa babu zunubi mafi girma irin zub-da-jini ba bisa haƙƙin Allah ba? Amma su na tayar da jijiyar wuya, don kada a yi zanga-zanga?
13. Me ya sa malamai ke kare ’yan siyasa da ake zargi da cin amanar dukiya? Kamar yadda su ka yi gungu lokacin badaƙalar Ganduje, su ka yi masa caffa da goyon baya, har da kwatanta shi da Aisha (RA) matar Manzon Allah, cewa yadda Allah ya wanke ta haka su ke sa ran Allah zai wanke shi daga zargin cusa Dollar?
14. Me ya sa hankalin malaman Arewa ke tashi da zarar an yi maganar zanga-zanga a lokacin mulkin APC?
15. Malaman Arewa sun manta sanda a baya ba sa cewa uffan idan aka yi bore, wadda ta fi zanga-zanga, inda ake far wa Kiristoci? Masu bore sun taɓa fasa kurkuku, aka kashe Kirista aka yanke kansa?
16. Ina malaman Arewa a duk lokacin da talakawa suka ɗauki doka ta kisa a hannunsu a kan talakawa Musulmi ko Kirista?
17. Sai za a yi wa gwamnatin APC sannan zanga-zanga da bore ke haramta?
18. Mutum nawa EFCC ta zarga da sace kuɗaɗen jama’a? Sun taɓa kira a ƙaurace wa irin waɗannan mutane?
19. Me ya sa ba a ganin su a gaba wajen kira a kan haƙƙin talaka? Amma su na gaba wajen kare muradun ’yan siyasa da mahukunta?
20. Me ya sa ba ka taɓa jin aikin hisba a kan attajiri da mahukunta ba, sai dai talaka kullum?
21. Shin àkwai gaba ne tsakanin malaman Arewa da talakawan Arewa?
Matuƙar malaman Arewa ba za su iya bai wa matasan Arewa amsoshin waɗannan TAMBAYOYI ba, haƙiƙa ya tabbata kenan talakan Arewa ba shi da babban abokin gaba sama da malamai saboda:
1. Sun kasa kare haƙƙin talaka a hannun mahukunta.
2. Ba su nema wa talaka haƙƙinsa ba, Amma su na ƙoƙarin danne shi kada ya fito ya nemi haƙƙinsa.
3. Sun nuna cewa, lallai ba sa son talaka, domin duk azabar da mahukunta za su yi masa babu ruwansu.
4. Sannan duk wani yunƙuri da talaka zai yi na neman mafita, za su danne talaka.
A ƙarshe, malamai su tuna zancen da su ke karantarwa cewa, “Mulki na iya ɗorewa da kafirci, amma mulki ba ya ɗorewa da zalunci.”
’Yan siyasa, malamai, masarauta da attajirai sun hadu sun tura talaka bango… To, lallai su ji tsoron ranar da talaka zai juyo baya. INNA RABBUKA LABIL MARSAD!!!
