Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta raba wa iyalan waɗanda ta’addanci ya shafa a ƙaramar hukumar Sabuwa da kuɗi Naira miliyan ashirin.
Mutanen kuwa sun haɗa waɗanda suka rasa rayukansu da waɗanda suka samu raunuka, sauran sun haɗa da waɗanda har ya zuwa yanzu sunan hannun ‘yan bindiga da wanda suka yi asarar dabbobi su.
Mataimakin na musamman ga waɗanda ta’addanci ya shafa da ‘yan gudun hijira Alhaji Sa’idu Ibrahim Danja ya raba wannan tallafi ya ce mutane 81 aka raba masu tallafi.
Ya bayyana cewa mutum 16 aka kashe a yayin da mutum 2 suka samu raunuka sai mutum 62 da ke hannun ‘yan bindiga.
Alhaji Sa’idu Ɗanja ya kuma sanar da cewa suma jami’an tsaron da suka rasa rayukansu a yankin sun samu Naira miliyan ɗaya kowanensu.
Mataimakin na musamman ya jaddada kuɗin gwamnatin Dikko Raɗɗa na shawo kan matsalar tsaro a wasu sassan jihar tare da tallafawa waɗanda abin ya shafa.
Shugaban ƙaramar hukumar Sabuwa Faruk Gatari a nasa jawabi ya yaba wa gwamna Dikko Raɗɗa da yadda yake tunkarar matsalar tsaro a jihar.
Ya kuma yi godiya a madadin waɗanda suka amfana da tallafin da kira ga iyalan waɗanda aka damkawa kuɗaɗen da su yi amfani da su yadda ya dace. Su dai waɗanda suka rasa rayukan su sun sami N200.000 kowanne su masu raunuka da waɗanda ake garkuwa da su sun sami N100.000 kowannen su da iyalansu suka karɓa.
