Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Ƙaramin Ministan Tsaro kuma tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya musanta zargin ta’addancin da wani sarkin ‘yan bindiga, Bello Turji ya yi masa, yana mai cewa ‘yan adawar sa ne ke yi masa sharri.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ta fito daga ofishin Ministan a ranar Lahadi.
A cikin wani faifan bidiyo da ya fitar a shafukan sada zumunta, Turji, shugaban ƙungiyar ɓarayin daji da ke gudanar da ayyukanta a arewacin Nijeriya, ya zargi Matawalle da rashin tafiyar da harkokin tsaro yadda ya kamata a lokacin da yake gwamnan jihar Zamfara.
Turji ya alaƙanta ƙaruwar ta’addanci a Zamfara da sauran jihohin arewa maso yammacin ƙasar da manufofin da gwamnatin Matawalle ta ɓullo da shi a lokacin yana gwamna.
A cikin faifan bidiyon, Turji ya ce, “Duk mutumin da ke zaune a Shinkafi, Zurmi, da Isa (Jihar Sokoto) ba zai iya musanta wannan ikirari ba. Akwai wasu gungun ‘yan fashin da tsohon gwamnan ya cuce su. Na kori ƙungiyar daga Shinkafi, na kashe shugabansu, Dudu, domin zaman lafiya a Shinkafi. Ƙungiyar na da makamai 200, amma daga baya gwamnan ya karɓe su (Yaran Dudu) a gidan gwamnati.
“Amma gwamnati ta gaza neman ƙungiyar ta miƙa makamansu. Wata ƙungiya da Bashari Maniya ke jagoranta tana da bindigogi sama da 300.”
Ya faɗi haka ne a lokacin da yake ikirarin kwace bindigogi 30 daga hannun ƙungiyar ‘yan bindiga ƙarƙashin jagorancin Bashari Maniya.
Sai dai da yake mayar da martani kan zargin da ake masa, Matawalle a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi ya bayyana ikirarin a matsayin mara tushe balle makama da ƙoƙarin ɓata masa suna.
Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Dayemi Saka, Jagorar Abokin Hulɗa a Lambert da Curtis, ta karanta a wasu sassan cewa, “An ja hankalinmu ga wani faifan bidiyo da aka yaɗa a shafin Ɗ da kuma Facebook wanda a ciki ake faɗi maganganu marasa tushe, ƙeta, ɓarna da ganganci. An yi wa mai girma ƙaramin ministan tsaro, Bello Muhammed Matawalle ƙazafi.
