Gwamnatin Tarayya na jan kunne a kan cewa ƴan ta’adda na iya fakewa da zanga-zangar da ake shirin yi domin kawo tashin hankali ko aikata ɓanna kamar yadda sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume ya faɗa.
Ya cigaba da cewa, zanga-zanga ba ita ce amsar halin da ake ciki ba na matsin rayuwa wanda ya tabbata shugaban ƙasa yana iya bakin ƙoƙarin shi ya shawo kai.
A wannam gaɓa ne, na ke kira da ‘yan Nijeriya da cewa su ƙara hakuri, komai zai wuce nan bada jimawa ba.
Yayi kira da ƴan Nijeriya masu shirya zanga-zanga da su zo ai zauna a tattauna dasu domin shawo kan matsalolin baki ɗaya. Yace wannan matsalolin abu ne da gwamnatin ta gada daga gwamnatin da ta shuɗe.
