GGSS Duka-wuya, Mariri da Bulukiya sun yi bikin ranar jawabai da raba kyautuka     

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano

Makarantun sakandare uku ne suka yi bikin mai kama da bajekoli na ranar jawabai da raba kyaututa ga haziƙ an ɗalibai na makarantun wanda ya ke nuna an kammala shekarar karatu ta 2024 lafiya kamar dai yadda rahotanni daga shugabanin makarantun da mahalarta tarurukan suka bayyana a wannan lokacin.

Malama Halima Ali Kabir, ita ce shugabar makarantar sakandire ta ‘yan mata, GGSS Dukawuya, ta ce wannan makaranta an buɗeta a ranar 21 ga watan Janairu, 2005 kuma wannan ne karo na farko da ma’aikatar ilimi ta ɗauki wannan makaranta a ɗaya daga cikin makarantun da za a yi wannan biki na ranar jawabai da raba kyaututuka ga haziƙ an ɗalibai wanda kuma abun anyi shi cikin gagarumar matsala wanda ya samu halartar iyaye da sauran manyan mutane da suka haka da iyayen ƙ asa ‘yan kasuwa da kuma shugabanni wanda har mai ba gwamnan Kano shawara kan ilimi Hon Tajuddeen Gambo tsohon Kwamishinan Ilimi ya samu halarta da kuma yin jawabi na ciyar da wannan makaranta gaba dai dai da manufar gwamnatin kano da Alhaji Abba Kabir Yusuf, na bunƙ asa ilimi a Jihar Kano baki ɗaya.

Shi kuwa Alhaji Ado Shuaibu, shugaban makarantar sakandire ta maza GSSS Mariri ya bayana wannan rana a matsayin ranar farinciki da ƙ arfafa gwiwa ganin yadda kwamishinan ilimi Hon Haruna Umar Doguwa, ya samu sahalewar gwamnan kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, wajen gyara da kuma inganta harkar koyo da koyarwa a makarantun kasandire kamar dai yadda mu muke gani a halin yanzu kuma muna kyakyawan zato cewa matsalolin wannan makaranta ta GSSS Mariri ta zo ƙ arshe da ikon Allah.

Hon. Kamaludden Abubakar Baba, mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso ne na ɗaya daga cikin manyan baƙi da ya bayana cewa gwamnatinsu ce kawai ta NNPP a Kano ta sa dokar ta ɓaci a ɓangaren ilimi don haka burin gwamnatin Abba, na ɗaya har na uku shi ne Ilimi.

Ita kuwa shugabar ƙungiyar shugabanin makarantun sakandire ANCOPSS ta riƙon ƙwarya Hajiya Uwani Balarabe, bayana gamsuwa ta yi akan yadda waɗanan makarantu ke gudanar da irin waɗanan bukukuwa wanda zai ƙ arama yara gwarin ƙ wiwa wanda zai garawa yara dagewa da karatu musammam ganin yadda hukumar makaranta ta ke samun haziƙ an yara tana basu kyaututuka masu armashi da ƙarfafa gwiwar ɗalibai        

GGSS Bulukiya wacce Malama Hannatu Ado Gwaram, ke shugabanta ta ce sun miƙa buƙatar samar da ɗakin karatu na lura da yadda ake futar da sauti kasancewar makarantar na koyar da harshen turanci Arabiyya da harshen Hausa shi ma harshe yanada ɗakin kula da sauti kamar yadda ake da ɗakin kimiya da fasaha kuma abun jin ɗaɗi shi ne kwamishinan ilimi na wancan lokaci wanda kuma shi ne ya kafa makarantar Hon Tajuddeen Gambo, ya zo taron a matsayin wakilin gwamnan Kano duk yaga matsalolin makarantar kuma tasan za a warwaresu kamar yadda ƙ udurin gwamnatin Kano ya ke akan ilimi.

Taron dai na makarantar GGSS Bulukiya ya samu halatar manyan baƙ i irinsu Sharu Mamuda Ali, shugaban ƙungiyar iyaye da malaman makaranta na Bulukiya sai shugaban ƙungiyar gatan makaranta SBMC Hajiya Ummi Alhassan ƙofar Ruwa, kuma shugabar mata ta jam’iyar NNPP a wannan yanki, sai Alhaji Auwalu Yalwa, Shugaban GSSS Dala Alhaji Tijjani Yusuf ɗan Mai Kunu, shugaban ƙungiyar dala ina mafita dake Kano da dai sauran baƙi da suka yi dogon jawabi kan yadda suke samun haɗin kan shugabnani wajen cigaban makarantar ta Bulukiya.

By ukarofi