Kamfanin lantarkin Kaduna ya warware saɓanin bashin harajin N600m da gwamnatin jihar

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Kamfanin raba wutar lantarki na jihar Kaduna (KAEDC), ya ce an warware saɓanin bashin harajin da ke tsakanin sa da gwamnatin jihar a ranar Litinin.

A ranar 2 ga watan Agusta ne, hukumar karɓar haraji ta jihar Kaduna, KADIRS ta garƙame hedikwatar kamfanin kan zargin bashin harajin Naira miliyan 600.

Shugaban hukumar, Jerry Adams ya ce sai da su ka samu umarnin kotu kafin su ka garƙame ofishin kamfanin.

Jim-kaɗan bayan haka ne, kamfanin ya sanar da katse samar da wuta ga Fadar gwamnatin jihar da wasu wurare mallakar gwamnatin kan bashin sama da Naira biliyan 2.9.

Sai dai a wata sanarwa da kamfanin ya fitar, ya ce an warware dukkannin matsalolin da ke tsakanin ɓangarorin biyu bayan da aka samu zama a lokuta mabanbanta da su ka haɗa da wakilai daga kamfanin da kuma gwamnatin jihar.

Darakta Manaja na kamfanin, Umar Abubakar Hashidu yi miƙa godiyarsa ga gwamnan jihar, Uba Sani; Darakta Manaja na kamfanin samar da wutar lantarkin jihar, Idris Aminu Idris; shugaban hukumar wutar lantarki, Aminu Abubakar Sulaiman da takwarorinsa da shugaban KADIRS da kuma wasu manyan ma’aikatun gwamnati a ƙoƙarinsu na sanya hannu wajen warware matsalolin.

By Babaji