Rumbun lantarki na ƙasa ya sake sauka

Spread the love

Rumbun lantarki na ƙasa ya sake sauka karo na biyar a cikin shekarar nan. Duk da hukumar TCN ba ta ce komai ba, kamfanin wutar lantarki na Abuja ya bada sanarwar, rumbun ya sauka da misalin karfe 2:55 a jiya litinin.

Amma sun ba kwatomominsu hakuri, cewar komai zai dawo dai dai.

Rumbun ya sauka karo na biyar kenan a wannan shekarar, inda a baya ya sauka a watannin Fabrairu,Aprilu da kuma Yuli.

By ukarofi