PDP ta dakatar da Suswam da wasu ‘yan jam’iyya a Benuwai

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jam’iyyar PDP a Jihar Benuwai ta dakatar da Sanata Gabriel Suswam da Terngu Tsegba da Richard Gbande da Terseer Tsumba da Farfesa Nicholas Ada daga jam’iyyar.

Haka kuma ta dakatar da shugabannin jam’iyyar na ƙananan hukumomin Apa, Gboko, Gwer-East, Katsina-Ala, Konshisha, Logo, Otukpo da Ukum.

A ranar Laraba ne dai jam’iyyar ta gayyaci waɗanda abin ya shafa, bisa zarginsu da aikata zagon-ƙasa da kuma cin amanar jam’iyyar.

Sammacin wanda ya nuna rashin jituwar da ke faruwa a cikin jam’iyyar a jihar, ya biyo bayan wani hari da wasu ɓatagari suka kai a sakatariyar jam’iyyar a jihar a Makurdi, inda rahotanni su ka ce wani shugaban jam’iyyar da aka dakatar, John Ngbede ya jagoranta.

An buƙaci waɗanda abin ya shafa su bayyana a gaban Kwamitin Ayyuka na Jiha (SWC) a jiya Alhamis da ƙarfe 10 na safe.

A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na jihar, Bemgba Iortyom ya fitar, ya ce kiran na da nufin tattaunawa da waɗanda aka gayyata a matakin farko da kuma yiwuwar kaucewa ɗaukar matakin ladabtarwa.

“Amma maimakon amsa gayyatar sulhun da aka yi musu, sai suka zaɓi hanyar ƙin bayyana a gaban kwamitin SWC kamar yadda aka bukƙata, inda wasunsu su ka riƙa fallasa jam’iyyar a fili suna zubar da mutuncin jam’iyyar da aka kafa.

“Halayensu na rashin jin daɗi ya ci karo da sashe na 58 na kundin tsarin mulkin jam’iyyar PDP (wanda aka yi wa gyara a 2017) don haka an dakatar da su daga jam’iyyar na tsawon wata ɗaya (1), kuma an umarce su da su bayyana a gaban kwamitin ladabtarwa a rana, wuri da lokaci da kwamitin zai sanar da su,” inji Iortyom.

By ukarofi