
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Yayin da zaɓen shugaban ƙasar Amurka ke cigaba da ƙaratowa, an sanar da sanya lokacin tafka muhawara na farko tsakanin Donald Trump da takwararsa Kamala Harris.
Tashar ABC ta ruwaito cewa cewa za ta haska muhawarar wacce za ayi tsakanin ƴan takaran biyu a ranar 10 ga watan Satumba kamar yadda ta wallafa a shafinta na X.
Hakan na zuwa ne bayan da Trump ya yi wasu kalumai a ranar Alhamis inda ya ce a shirye ya ke ya fafata da abokiyar karawar tasa a lokuta da dama kafin lokacin zaɓen wanda za a yi acikin watan Nuwamba.
A ranar Alhamis hallau, a yayin wani taro a Michigan, Harris ta tabbatar da cewa za ta halarci muhawarar, ta na mai nuna cewa ta shirya tsaf wajen tunkararsa a kowane mataki na gwabzawa.
