Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya jaddada irin aikin da shugaba Tinubu ya ke yi domin ganin matasa sun samu abin yi musamman ta hanyar sana’o’i da suke sha’awar yi.
Hakan ya fito ne a wata sanarwa da babban mai ba mataimakin shugaban ƙasan shawara a harkokin yaɗa labarai Stanley Nwkocha ya fitar, inda yace, shugaba Tinubu ya ɗauki matasa da muhimmanci ganin yadda ya ke ta fito da tsare-tsare da naɗe-naɗe duk domin matasa.
Kashim yayi wannan maganar ne a ranar Juma’a lokacin da ya karɓi baƙuncin matasan jami’iyyar APC tare da shugaban su Mr Dayo Israel a wata ziyara da suka kai fadar shugan ƙasa.
Ya cigaba da cewa, matasa sune jigon ko wacce ƙasa don haka shiyasa shugaba Tinubu ya ke dagewa ganin bai ba matasa kunya ba.
Kashim ya yabawa matasan APC ɗin da wannan ziyarar da suka kawo mashi.
A jawabin shugaban matasan, Dayo Israel, ya godewa mataimakin shugaban ƙasar da irin jajircewarsa wajen ganin Nijeriya ta samu cigaba musamman ta ɓangaren matasa.
Ya bayyana cewa, dalilin kawo ma mataimakin shugaban ƙasar ziyara shine domin su jaddada goyon bayan su ga tsare tsaren gwamnatin.
A cewar shi, matasan APC din suna da jadawalin aiki na shekara huɗu domin ganin sun taimaki matasan Nijeriya.
Dayo Israel daga ƙarshe ya roƙi mataimakin shugaban ƙasar samun halartar taron su na matasa da za a gudanar ba da jimawa ba.
A tare da shugaban su, akwai mataimakin matasan Jamalu Kabiru, sai jagororin yankuna daban daban na ƙasar.
