Gwamnan Bauchi ya nemi agajin Tinubu akan titin Kano-Maiduguri da ambaliya tai awon gaba dashi

Spread the love

Wani ruwan sama da aka yi mai ƙarfin gaske ya yi awon gaba da wani sashen titin Maiduguri-Kano.

Wannan ya auku ne a ƙauyukan Malori da Guskuri duk a cikin ƙaramar hukamae Katagum da ke jihar Bauchi.

Yayin ziyarar gani da ido, gwamnan ya roƙi gwamnatin tarayya da ta zo ta kawo agaji da gaggawa domin titin ya na da matuƙar muhimmanci. Domin shine ya haɗa Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.

Yace idan ba suyi ba, dole su ɗau mataki na wucin gadi kamar yadda su kayi a bara da wani abu makamancin haka ya faru.

A wani labarin mai kama da wannan, hukumar ba da agajin gaggawa da Jihar Neja ta shaida cewa aƙalla mutum 20 sun rasa rayukansu a sakamakon ambaliyar ruwa da ta faru a
Ƙananan hukumomi 10 a faɗin jihar.

By ukarofi