Jam’iyyar PDP a Jihar Katsina ta maka uwar jam’iyyar ta ƙasa a kotu.

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Rikici ya ɓarke a jam’iyyar adawa ta PDP reshen Jihar Katsina biyo bayan zaɓen jagororin jam’iyar a matakin gundumomi da ƙananan hukumomi da ya gudana.

Tsagin jam’iyyar ƙarƙashin shugabancin Mustapha Inuwa suka maka uwar jam’iyyar ta ƙasa a kotu.

Suna buƙatar kotu ta tsaida zaɓen bisa zargin hana mutanen su da yawan su yakai 7,000 sayen takardar cikewa na shiga zaɓen.

Sun zargi tsohon ɗan takarar gwamna a zaɓen 2023 sanata Yakubu Lado Ɗanmarke da mallake jam’iyyar.

Sun kuma zarge shi da yiwa jam’iyyar zagon ƙasa da haka yasa jam’iyyar ta kasa taɓuka komai a zaɓuɓɓukan da suka gabata.

Lauyan tsagin jam’iyyar, Mustapha shitu ya bayyana zaɓen shugabannin jam’iyyar da ya gudana a jihar a matsayin haramtacce, da tuni maganan tana kotu.

” An riga an sanar da uwar jam’iyyar ta ƙasa ta hannun babban lauyan su, Godwin Uche biyo bayan ƙarar da muka shigar na ƙalubalantar zaɓen”

Lauya Akinlaja ya kara da cewa suna wakilatar mutane 7,000 halastattun ya’yan jam’iyyar da aka hana su sayen takardar cikewa na shiga zaɓen da yace haramtacce ne.

Ya ce idan ƙara na kotu, to dole ne ɓangarorin biyu su dakatar da yin wani abu da ya danganci wannan sai an gama Shari’a.

Sai dai uwar jam’iyyar ta jihar wanda tana tare da tsagin lado Ɗanmarke ta jagoranci gudanar da zaɓuɓɓukan a faɗin jihar.

A karamar hukumar Rimi,Tijjani Mashasha wakilin uwar jam’iyyar ta jihar ya gudanar da zaɓen akan sa idon hukumar zaɓe na ƙasa da jami’an tsaro.

Wakilai guda 30 ne suka zaɓi shugabannin jam’iyyar guda 18 a karamar hukumar da kuma zaɓen wakili da zai wakilci ƙaramar hukumar a zaɓen shugabanin ƙungiyar na ƙasa.

Mashasha ya faɗawa manema labarai bayan kammala zaɓen, sun gudanar da zaɓen a matakin gundumomi kafin a zo na ƙaramar hukuma.

A cewarsa sun gudanar da zaɓen cikin lumana da kwanciyar hankali,kuma iya saninsu ba su sami wani umarni daga kotu ba na tsayar da zaɓen.

Yace fatan su jam’iyyar ta PDP ta sake karɓar mulki a matakin jiha da ƙasa baki ɗaya.

By ukarofi