NYSC ta magantu kan fara biyan masu hidimar ƙasa Naira 70,000

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Hukumar kula da ɗalibai masu yi wa ƙasa hidima, NYSC ta ƙaryata labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa ƴan hidimar su faɗaɗa asusun bankunansu ta yadda za su ke ɗaukar sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000.

Hukumar ta bayyana hakan ne cikin wata takarda da Darakta hulɗa da jama’arta, Eddy Megwa ya fitar inda ya ce jawabin ba gaskiya ba ne, ya na mai cewa babu wani umarni daga wata hukuma kan fara biyan ƴan hidimar ƙasar Naira dubu saba’in ko batun faɗaɗa asusun nasu.

Ya kuma yi kira ga ƴan hidimar da su ƙaurace wa masu yaɗa labaran ƙarya da ke karkatar da tunanin al’umma da wasa da hankulansu.

“Masu hidima, iyaye da sauran mutanen ƙasa su sani babu wani umarni daga wani ɓangare na gwamnati da aka samu kan batun biyan kuɗi.”

Ya ƙara da cewa, ƴan hidimar sun san hanyar da su ke karɓar saƙo don haka ya ke kira gare su da su yi watsi da labarin.

By Babaji