‘Yan bindiga sun yi wa sojoji kwanton ɓauna a Sokoto, sun kashe da dama

Spread the love

Wasu ‘yan bindiga sun yi wa sojoji kwantan ɓauna a ƙaramar hukumar Gudu da ke Sokoto, inda su ka samu nasarar kashe sojoji huɗu da jikkata wasu guda biyu.

Ɗan majalisar jihar mai wakiltar Gudu shi ya tabbatar da faruwan wannan al’amari inda ya ƙara da cewa sun ƙona motocin sintiri guda biyu na sojojin.

“Gaskiya ne, ‘yan bindiga sun yi wa sojojin da ke sintinri a kan titin Kukurau-Bangi kwantan ɓauna inda su ka samu nasarar kashe huɗu daga cikin sojojin, yayin da wasu guda biyu suka jikkata”

Ɗan Majalisar ya cigaba da cewa wannan labari marar daɗi ne, inda har an sanar da gwamnan Sokoto an ƙaro jami’an tsaro a wannan yankin.

Wani mazaunin yankin yace, sun ga lokacin da ‘yan bindigan ke wucewa a saman baburan su da za su kai 20, ba wanda suka taɓa a yankin namu sai dai bayan wucewar su munji harbin bindiga.

By ukarofi