Shettima ya soki shekara takwas na gwamnatin Buhari

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Shugaban ƙungiyar matasa mashawarta na Arewa (AYCF), Yarima Shettima ya fassara shekaru takwas da tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya ɗauka ya na mulkin Nijeriya a matsayin asara ga Arewa da ma ƙasa baki ɗaya.

Ya na mai cewa shugabannin bayan sun nuna halin ko-in-kula ga Arewa na tsawon lokaci wanda hakan ya sa aka tura al’ummar yankin zuwa ga bango.

Shettima ya faɗi hakan ne a yayin wata hira da jaridar ‘Vanguard’ a ranar Lahadi inda ya ce zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi a Nijeriya ya fusata al’umma, ya na mai cewa matuƙar shugabanni ba su ɗauki mataki ba, to za a yi wanda zai haɗiye kowa a nan gaba.

Haka nan, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gaji matsalolin Nijeriya da damuwar da al’umma suka tsinci kansu.

Har’ilayau, ya kuma soki rahotonnin da ke cewa musabbabin abin da ya fusata al’ummar Arewa shi ne batun raba muƙamai da wasu ke ganin an mayar da Arewa saniyar ware, ya na mai cewa matsalolin yankin ya wuce batun raba muƙamai.

By Babaji