Shugaban ƙungiyar Arewa Consultative Forum Shetima Yerima, a wata hira da yayi ya bayyana cewa ‘yan Arewa sun fito zanga-zanga ne a dalilin yunwa da ƙuncin rayuwa da ke damun yankin.
Hakan ya samo asali ne tun daga irin riƙon sakainar kashi da masu mulki su ka yi wa matsalolin al’ummar yankin.
Ya cigaba da faɗa cewa, idan muka duba ko a rabon muƙamai, ba a ba ‘yan Arewa sosai ba, waɗanda kuma a ka ba, ba su da mu’amala da mutane har su san halin da mutane ke ciki.
Batun zargi da ake lokacin da a ka gudanar da zanga-zangar #ENDSARS “yan Arewa ba su shiga ba, wannan ya bayyana cewa zanga-zangar ‘yan yahoo ce, don haka ‘yan Arewa ba wannan ne matsalar su ba. Yunwa da matsin rayuwa sune matsalar Arewa ba #ENDSARS ba.
A ƙarshe yayi kira da shugabanni su yi abinda ya dace domin dawo da martabar yankin ta fannin tsaro da tattalin arziki.
