Ɗaga tutar Rasha yayin zanga-zanga a mahangar shari’a 

Spread the love

Daga  AHMAD DAN-WUDIL

Zanga-zangar yunwa da ke ci gaba da gudana a faɗin ƙasar nan na neman sauya salo, duba da yadda take haifar da cece-kuce, musamman game da sabon salo da aka zo da shi wanda ke ƙoƙarin sauyawa zanga-zangar suna, wato ɗaga tutar Rasha da wasu daga cikin masu zanga-zangar ke yi. 

Yana da matuƙar muhimmanci a yi nazarin wannan lamari ta mahangar kundin tsarin mulkin Najeriya da tanade-tanaden doka ta yi kan yin hakan.

Sashe na 39 da na 40 na daga kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi ‘yancin faɗin albarkacin baki, tare da damar gudanar da taro ko kuma gangami na lumana. Waɗannan dokokin suna da muhimmanci a cikin tsarin mulkin dimokuraɗiyya, don tabbatar da dama ga ‘yan ƙasa na iya bayyana kokensu ba tare da tsoron danniya ko hukunci ba. 

Duk da haka, yana da matuƙar muhimmanci a fahimci cewa, waɗannan dokokin ba iya haka suka tsaya ba. Kamar yadda sashe na 45 (1) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya bayyana, ana iya tauye waɗannan ‘yancin  (na doka ta 39 da 40) don kare haƙƙin jama’a, tsaron lafiyar jama’a, zaman lafiyar jama’a, ɗabi’ar jama’a, ko don manufar kare haƙƙoƙin ’yancin wasu.

Duk da cewa, babu wata doka takamaimiya da ta haramta ɗaga tutar wasu ƙasashe, kamar tutar ƙasar Rasha yayin gudanar zanga-zangar, hakan ba yana nufin ba bu laifi ayin hakan, maimakon haka, akan yi duba da irin sakamakon da yin hakan zai haifar.

Wannan hukunci ( na ɗaga tutar) ka iya janyo harzuƙawa ko bacın rai, wanda zai iya kai wa ga janyo rashin kwanciyar hankalin jama’a ko kuma ɓata alaƙar Najeriya da ƙasashen waje. Don haka ana iya kallon hakan a matsayin barazana ga tsaron ƙasa.

Sashe na 50 da na 51 na kundin laifuffuka sun haramta tayar da tarzoma, wanda ya haɗa da ayyuka, jawabai, ko wallafe-wallafen abubuwan da za su haddasa tsana, rashin yarda ga gwamnati a baynar  jama’a.

ɗaga tutar Rasha a cikin zanga-zangar zai iya shiga cikın wannan. Don haka, mutanen da ke da hannu a irin waɗannan ayyukan za su iya fuskantar tuhumar tayar da zaune tsaye.

Gargaɗi:

Duba da waɗannan abubuwa, Ina kira ga mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro da sauran shugabannin tsaro su sa baki domin daƙile duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya. Bugu da ƙari, ina kira ga ‘yan ƙasa da su daina ɗaga tutocin ƙasashen waje yayin zanga-zangar don guje wa hukuncin shari’a. 

Mutanen da aka samu da keta kowacce daga dokokin da aka lissafa, za su iya fuskantar mummanan hukuncin shari’a, ciki har da tuhumar tayar da zaune tsaye.

Dan-wudil masanin shari’a ne, ya rubuto daga Abuja

By ukarofi