Tinubu ya amince da ƙarin albashin ma’aikatan shari’a da kaso 300%

Spread the love

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince ya sanya hannu a kan dokar da zata ƙara wa ma’aikatan shari’a albashi da kusan kaso 300%. Wannan sanarwar ta fito daga bakin Sanata Lado, wanda shine mai ba shugaban ƙasa shawara a kan harkokin majalisa.

Idan ba mu manta ba, a watan Yuni, shugaban ƙasa ya aikewa majalisa kundin dokar kan batun ƙarin albashin ga ma’aikatan shari’a a faɗin tarayya da jihohi. A cikin watan majalisar da zartar da doka kuma ta aikewa shugaban domin sanya hannu.

Lado ya bayyana cewa, yin haka yana nuni da irin jajircewar da Shugaban ƙasa ya ke yo domin walwalar ma’aikata a faɗin ƙasa.

By ukarofi