An buƙaci Gwamnan Katsina ya dakatar da shirinsa na rushe kasuwar Funtua

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina.

Ƴan kasuwan da ke babbar kasuwar garin Funtua, sun yi kira ga gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Raɗɗa da ya dakatar da shirinsa na rushe kasuwar.

Sakataren yaɗa labarai na kungiyar ƴan hatsi a kasuwar, Shehu Ɗahiru Mai-Wada ya yi wannan kira a garin Funtua inda ya ce wannan mataki na gwamnan zai jefa da dama daga cikin ƴan kasuwa cikin halin ƙunci.

Ya kara da cewa, mafi yawancin ƴan kasuwan zasu rasa matsugunin wajen da zasu rinƙa harkokin kasuwancinsu.

Mai-Wada ya ƙara da cewa, tun da aka ɗauki tsawon lokaci ana kulle a lokacin ciwon Koriya ya zuwa yanzu ba su farfaɗo ba, ga ɗinbin bashi ya yi mu su yawa.

A maimakon haka, ya ce gwamnati ta samu wani fili a wajen gari ta gina kasuwar domin idan yanzu aka rusa kasuwan da suke ciki basu san inda zasu ba.

Sakataren yaɗa labaran ya kuma yi kira ga gwamnan da ya tallafa wa ƴan kasuwan domin su samu damar miƙewa, saboda yawancin su sun durƙushe kasancewar ba kasuwa.

A kwanakin baya ne, Dikko a wata ziyara da ya kai a babbar kasuwar, ya sanar da cewa gwamnatinsa zata rushe kasuwar domin ta gina wata sabuwa, ya na mai cewa hakan ya zama dole domin a faɗaɗa kasuwar da yi ma ta gini irin na zamani.

By Babaji