Hukumar NNPC ta gaza fara aiki a matatar Fatakwal a karo na shida bayan bada tabbacin yin haka a faɗin shugaban ta Mele Kyari a watan Yuli.
Kyari ya bada wannan tabbacin ne a gaban majalisa, in da ya ba ‘yan majalisar tabbacin cewa kafin ƙarshen shekara Nijeriya za ta daina shigo da mai, sai dai ta fitar.
A yayin da a aka tuntuɓi hukumar NNPC kan yiyuwar fara aikin matatar Fatakwal, mai magana da yawun hukumar Olufemi Soneye ya ce suna kan aiki domin ganin haka ya faru, daga nan bai sake amsa wasu tambayoyin da aka mai ba.
Idan ba mu manta ba, tun daga Disamba 2023, hukumar NNPC ta bada lokaci daban-daban a kan cewa matatun man ƙasar za su dawo aiki amma har yanzu sun gaza cika wannan alƙawarin.
