
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce har yanzu a gidan haya ya ke zama a Abuja wanda nda ya samu haka ne a sanadiyyar tasirin horo daga ƙungiyar ɗalibai musulmai ta Nijeriya, MSSN.
Shekarau, wanda tsohon ministan ilimi ne, ya ce bai taɓa tattauna batun samun wani kaso da kowane ɗan kwangila ba a lokacin da ya ke gwamna.
A lokacin da ya ke magana game da batun mutuntaka a taron manema labarai gabannin bikin cikar shekara 70 na MSSN da za a fara a ranar 12 ga watan Oktoba, 2024, Shekarau ya ƙalubalanci duk ƴan kwangilar da ya yi aiki da su a tsawon shekaru 44 cewa su faɗa idan ya taɓa tambayar su ko karɓar wani kaso daga gare su.
A matsayinsa na shugaban kwamitin shirye-shirye na ƙungiyar, Malam Shekarau ya yaba wa ƙoƙarin ƙungiyar na inganta rayuwarsa ta fuskar addini da ma wanin sa.
Ya kuma ce har zuwa lokacin da ya kammala wa’adinsa na biyu a shekarar 2011, bai mallaki gida na kansa ba.
“Na biyu, babu wani daga cikin kwamishinoni na da ya taɓa kawo mun Naira ɗaya da sunan tukuici daga wani ɗan kwangila.”
Haka nan, “babu wani shugaban ƙaramar hukuma a lokacin shekara takwas da na yi a mulki da ya taɓa kawo mun Naira ɗaya. Kuma ban taɓa taɓa mu su wani abu daga cikin kasafinsu ba”, inji shi.
