


Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana makarantar kwalejin tarayya reshen ilimin fasahar koyarwa (FCET) a matsayin zaure da ke samar da ƙwararrun malamai a makarantu a faɗin jihar.
A ranar Laraba ne shugabannin majalisar FCET suka kai ziyara wa gwamnan a Fadar gwamnatin jihar da ke Gusau.
Wata sanarwa daga mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ta ce ziyarar wani nau’i ne da ke nuna kusanci tsakanin gwamnatin da kuma majalisar tare da ƙarfafa alaƙa a tsakanin su.
A lokacin da ya ke magana, gwamna Lawal ya marabci mambobin majalisar tare da nuna muhimmancin ba ta cikakken goyon baya don bunƙasa cigaban ilimi a faɗin jihar.
“Ina so na fara da cewa, mutanen jihar Zamfara sun amfana sosai da makarantar kwalejin tarayya ta fasahar koyarwa da ke Gusau. Bari na bayyana ƙarara; kimanin ƴan uwana mata biyar ne su ka kammala karatu a FCET.”
Ya kuma ce, “a shekarar da ta gabata na sanar da dokar kulle ga ɓangaren ilimi saboda ƙalubalen da ke tattare da shi. Sama da shekara uku kenan da tsohuwar gwamnati ta gaza biyan kuɗaɗen jarrabawar NECO da na WAEC wanda ba a so hakan ba. Saidai, mun biya bashin wanda yanzu hakan ya zama tarihi”, inji Lawal.
Dauda Lawal ya ƙara da cewa, su na ƙoƙari wajen ganin kowane ɗa ya samu ilimi mai nagarta, ya na mai cewa a yanzu haka su na gina makarantu da gyara wasu da adadinsu ya kai 290 a faɗin jihar.
A wannan mataki ne FCET ke da muhimmiyar rawa da ta ke takawa wajen inganta harkar koyarwa wanda hakan taimaka wa ɓangaren ilimi ne a faɗin jihar.
