
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Hukumar Kwastom, NCS ta ce umarnin da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar na shigo da kayan abinci ba tare da biyan haraji ba bai kunshi shigo da hatsi ba ta kan iyakokin ƙasa a Nijeriya.
A shekarar da ta gabata ne gwamnatin shugaba Tinubu ta sanar da janye tallafin man fetur wanda hakan ya yi sanadiyyar tashin gwaoron zabi ga farashin kayan abinci da kuma karya darajar Naira wadda kasuwanci duniya ke sarrafata.
Hakan ya shafi shinkafa wadda ta na ɗaya daga cikin abincin da mafi yawancin ƴan Nijeriya ke amfani da shi inda a yanzu farashin buhu mai nauyin kg50 ya kan kai Naira dubu 60 zuwa 80 la’akari da inda mutum ya ke a faɗin ƙasar.
Akan haka ne Shugaba Tinubu ya bayar da damar shigo da shinkafa, wake, fulawa da sauransu.
Wata takarda daga ofishin mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ta hakaito maganar Ministan Noma, Abubakar Kyari inda ya ce “Mista Tinubu ya amince da shigo da kayan abinci na tsawon kwana 150 ba tare da biyan haraji ba, ciki har da; masara, shinkafar da ba a ɓare ba, fulawa da wake.”
A ranar 15 ga watan Agusta ne Kwastom ta sanar da batun shigowa da kayan abinci ba tare da biyan haraji ba cikin wata sanarwa da ta fitar inda ta ce tsarin ya fara aiki ne a ranar 15 ga watan Yuli yayin da zai ƙare a ranar 31 ga watan Disamba, 2024.
A lokacin da ya ke magana, shugaban hukumar, Bashir Adeniyi ya ce babu abin da ya canja game ga batun shigo da shinkafa, ya na mai cewa tsarin dokar ya bai wa masu filin noma shinkafa ne kaɗai damar shigowa da ita ba tare da biyan haraji ba.
