Ranar Matasa ta Duniya: Cigaba da ƙalubalen da matasanmu ke fuskanta

Spread the love

Daga IMAM HASSAN IMRAN

Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanya ranar sha biyu ga watan Agusta na kowacce shekara, don ta zama Ranar Matasa ta Duniya. A bana, bikin ranar ya mayar da hankali ne wajen kwaɗaitar da matasa muhimmancin amfani da fasahar sadarwa ta zamani, domin samar wa al’umma cigaba da kuma jan hankalin su akan duk abin da zai haifar da matsaloli ko kuwa tada zaune tsaye.

Abu ne da muka sani, matasa su ne makamashin kowacce al’umma. Haka zalika, su ne jijiyar bishiyar kowacce al’umma. Idan jijiyar ta inganta, al’umma za ta samu cigaba da wadataccen zaman lafiya. Amma idan ta kasance akasin haka, al’umma za ta fuskanci barazana, matsaloli da kuma tashe-tashen hankula. Samartaka lokaci ne na ƙarfi; lokaci ne da kowanne matashi da matashiya ke ji da ƙarfi a jikinsu. Don haka, Ubangiji ya aiko dukkan annabawa da manzanni da saƙonnin shiriya ga al’umma a lokacin samartakarsu. Saboda haka, samartaka lokaci ne da ake buƙatar amfani da ita ta hanyar da ta dace domin amfanar da al’umma.

Amma abin takaici kuma abin haushi shi ne yadda wasu matasa ke amfani da samartakarsu ta hanyar ɓata lokutansu akan abubuwan da ba za su haifar musu  da ɗa mai ido ba. Waɗannan abubuwan sun ƙunshi rashin kula da neman ilimin zamani da kuma na addini, harkar daba da sara-suka, yankan aljihu da sace-sace, da kuma tu’ammali da miyagun ƙwayoyi. Harwayau, matasa da dama na zaman kashe wando saboda rashin ayyukan yi, ko kuma kwaɗayin samun aikin gwamnati mai maiƙo, sun ɓuge da zama ƴan kanzagin ƴan siyasa da masu kuɗi, suna yi musu maula a shafukan sada zumunta wajen aibata juna, zage-zage da kuma yaɗa jita-jita da labarun ƙarya. Duk da kasancewar akwai gurɓatattun matasa, haka zalika akwai matasa da suke kan gaba wajen samar wa al’ummarsu abubuwan cigaba. 

A makon da ya gabata, jaridu sun ruwaito labarin wani matashi a garin Kano da ya ƙirƙiro wayoyin cajin wayar salula (USB Cable) wanda za a iya da su wajen cajin waya da naura mai ƙwaƙwalwa (tablets). Wannan labari ne mai daɗi, kuma abin yabawa ne. Ire-iren waɗannan matasa masu amfani da fasahar zamani na da yawa a Arewa da sauran yankunan ƙasar nan, amma basa samin karfin giwar da kuma mai talafa masu ba, shi yasa wasu kirkiran tasu take mutuwa kuma bata yaɗuwa yanda ya kamata. Da irin wannan halin, ta yaya zamu samar wa yankunan tamu cigaba ta zamani?

A ganina, daga cikin abubuwa da suke janyo durƙushewar fasahar matasa shi ne, jahilci da kuma rashin ilimi kan cigaban da fasahar za ta kawo a yankunan mu da kuma yadda za ta samar da ayyuka da bunƙasa tattalin arziƙin yankinmu na Arewa da kuma ƙasarmu bakiɗaya. Waɗanda ke riƙe da madafan iko da masu hannu da shuni sun fi tallafawa harkokin sharholiya da bukukuwa marasa amfani. Suna kashe maƙudan kuɗaɗe akan harkokin da ba za su kawo cigaba ga al’ummar mu ba sai dai   kawo talauci da kuma lalacewar tarbiyya.

Matasa su sani cewa akwai abubuwa da yawa da za su amfana da su ta hanyar fasahar zamani kamar ilimin zane-zane da ƙawata kaya (Graphic design) da kuma tallafawa kasuwanci da samar da manhajoji (Online marketing) da sauran su. Dukkan waɗannan mutum na iya koya a wayarsa musamman ta manhajar YouTube da sauransu. Kowanne ilimi na da matuƙar amfani, kuma mutum na iya dogaro da su a matsayin sana’a.

A ƙarshe, matasa su ɗaura damarar tashi su nemi ilimin zamani da kuma na addini. Haka kuwa su yi riƙo da kyawawan ɗab’u da za su ƙara haɗa kawunan al’umma, fahimtar juna da kuma samar da zaman lafiya. Matasa su guje wa zaman kashe wando da maula, su nemi sana’ar dogaro da kai. Babu abinda ya fi tashin hankali ka ga matashi ya wayi gari ba shi da wajen zuwa ko wajen neman ilimi ko sana’ar hannu. Irin waɗannan matasa abin tsoro ne kuma barazana ne ga al’umma, domin zaman kashe wando yana haifar da kowacce sharri da kuma munanan halaye. Haka kuwa, matasa su guje wa dukkan abinda ba zai kawo cigaba ga yankinsu ko al’ummar su ba. Su yi hannun riga da miyagun ƙwayoyi domin basu da wani amfani face halaka. Masu madafun iko da masu hali a cikin mu su taimaka wajen yaɗa fasaha da ƙirƙirar abubuwan da al’umma za ta samu cigaba mai ɗorewa.

Allah Ya kawo mana sauƙin rayuwa ya kuma shirya mana matasanmu. Amin.

Imam Hassan Imran ya aiko mana da wannan nasiha ne daga Jos, kuma za a iya samunsa kan lambar waya 09059323221

By ukarofi