Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Makarantun firamare na gwamnati a faɗin Nijeriya na ƙara taɓarɓarewa duk da cewa akwai kuɗi biliyan N54.9 na kuɗaɗen Hukumar Kula da Ilimin Bai ɗaya (UBEC) da gwamnatocin jihohi ke ci gaba da yin amfani da su.
Wannan sakaci da ake ci gaba da yi ya sa iyaye a garuruwa da dama na Nijeriya ke mayar da ’ya’yansu daga makarantun gwamnati zuwa makarantu masu zaman kansu saboda taɓarɓarewar ababen more rayuwa da rashin ingancin koyarwa da makarantun gwamnati.
Yayin da wasu gwamnatocin jihohin ke ikirarin ba da fifiko kan ilimin al’umma, rahotanni sun nuna cewa ya zuwa watan Maris ɗin shekarar 2024, jihohi kusan 26 da babban birnin tarayya Abuja sun kasa samun Naira biliyan 54.9 na kuɗaɗen UBEC da aka ware domin inganta ilimi.
Waɗannan kuɗaɗen, waɗanda aka tsara don haɓaka ilimi da rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, samun su ya ci tura.
Wata takarda da Daraktan Kuɗi da Akanta na UBEC, Adamu Misau ya sanya wa hannu, ta tabbatar da cewa har yanzu ba a samar tallafin karatu na naira biliyan 54.9 ga jihohi ba.
Rashin bayar da gudunmawar da gwamnatocin jihohi suka yi ga UBEC ya kawo cikas ga ci gaban makarantun gwamnati.
Ya zuwa watan Maris ɗin shekarar 2024, jihohi 26 da babban birnin tarayya Abuja sun shigar da naira biliyan 32.5 kawai ga hukumar ta UBEC, matakin da ya dace don samun kuɗazen da gwamnatin tarayya ke rabawa kowace shekara da nufin bunƙasa ilmin a matakin farko a faɗin ƙasar nan.
Oluwadare Kolawole, mataimakin daraktan ƙungiyar kare haƙƙin jama’a da tattalin arzikin ƙasa (SERAP), ya soki gwamnatocin jihohi da gazawar su, inda ya jaddada cewa kuɗazen da UBEC da ba a yi amfani da su ba, an yi su ne domin samar da muhimman ababen more rayuwa da biyan albashin malamai.
Kolawole, ya jaddada muhimmancin tushen ilimin firamare wajen tsara makomar zamantakewa da siyasa da tattalin arzikin al’umma.
