



Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
A ranar Talata ne gwamanan Zamfara Dauda Lawal Dare, ya ƙaddamar da raba taki tirela 135 ga manoma a ƙananan hukumomi 14 na faɗin jihar.
An gudanar da hakan ne a Ma’aikatar noma na jihar a ƙoƙarin gwamnan na haɓaka ayyukan noma a jihar.
Wata takarda da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce buhu 81,000 kyauta ne ga manoma 40,500 a kowace ƙaramar hukuma ta jihar.
Hakan kuma wani ɓangare ne na jaddada ƙoƙarin gwamnatin Dauda Lawal a Zamfara na bunƙasa harkokin noma ta hanyar tallafa wa manoma don inganta amfanin da su ke samarwa.
Kazalika, gwamnan ya kai ziyara baki ɗaya ƙananan hukumomin a watannin baya da su ka gabata inda ya raba taki da wasu kayan amfanin gona ga manoma da ke karkashin shirin NG-‘CARES programme’.
Ya ƙara da cewa, za su cigaba da ƙoƙarin tabbatar da cewa an samu gagarumin nasarar a ɓangaren noma ta hanyoyin da suka dace a faɗin jihar.
Bugu da ƙari, gwamnan yayi kira ga manoman da su yi amfani da taki ta hanyoyin da su ka dace, ya na mai yi musu alƙawarin cigaba da tallafa musu.
