Tsohon kocin Super Eagles, Salisu Yusuf ya karɓi aikin horar da Barau FC

Spread the love

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC ta sanar da ɗaukar tsohon kocin Super Eagles, Salisu Yusuf a matakin sabon wanda zai horar da ita.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar daga jami’in yaɗa labaran, Ahmad Hamisu Gwale ta ce kocin ya ratta hannu kan yarjejeniyar kaka ɗaya a gaban shugaban Barau FC, Jakada Ibrahim Shittu Chanji.

Barau FC ta ɗauki Yusuf ne, saboda da ƙwarewa da gogewar da yake da ita a tamaula, domin ya kai ƙungiyar firimiyar Nijeriya daga gasar rukunin farko a kaka mai zuwa.

Yusuf ya horar da ƙungiyoyi da dama ciki har da Kano Pillars da Enyimba da El-Kanemi Warriors da kuma Enugu Rangers, ya san gasar tamaula ta kasar ciki da waje.

Haka kuma ya yi mataimakin kociyan tawagar Nujeriya ƙarƙashin Stephen Keshi daga baya ya karɓi aikin riƙon ƙwarya, wanda daga baya aka damƙa masa jan ragamar Super Eagles a Oktoban 2021.

By ukarofi