DAGA MUKHTAR YAKUBU
A ƙoƙarin ta na samar da ayyukan yi ga matasa domin su dogara da kansu, Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin Hukumar tace finafinai da ɗab’i ta shirya taro na wuni biyu ga kurame masu harkar fim domin koyar da su da kuma wayar da kansu a kan sana’ar fim ta yadda za su samu cin gajiyar sana’ar ta su.
Taron wanda aka gudanar da shi a ranar Litinin da talata 19 zuwa 20 ga Agusta 2024 an gudanar da shi ne a ginin gidan Talbijin na ARTɓ Kano da ke kan titin Maiduguri a Unguwar Hotoro a Kano, ya samu halartar kurame masu sha’awar harkar daga sassa daban daban na Jihar Kano.
Tun da farko da yake Jawabi a wajen buɗe taron, Shugaban Hukumar tace finafinai da ɗab’i ta Jihar Kano Abba El-Mustapha ya bayyana cewa,
“Manufar shirya wannan taro da za a yi wuni biyu, shi ne wayar da kai da kuma ilimintar da kurame masu harkar fim, da kuma koyar da su yadda harkar fim take a ilmance kamar yadda ya kamata a yi kowacce sana’a cikin ilimi da kuma ɗora su a kan yadda harkar take tafiya da zamani.”
Ya ci gaba da cewa ” Waɗannan bayin Allah masu buƙata ta musamman, wato kurame, sun zo gare ni a ƙungiyance, mun zauna mun tattauna, kuma na ga irin yadda suke shirya ‘yan gajerun finafinai na labarai minti biyu zuwa uku a waya. Kuma sai abin ya ƙayatar da mu a matsayin mu na hukuma, muka ga cewar ya kamata mu janyo su, su ma su zo a dama da su a cikin wannan masana’anta ta shirya finafinai. Kuma Allah masani, duk abin da ka saka ilimi a cikin sa, za ka ga cewar yana bunƙasa tare da ƙara haɓaka.
Abin lura a nan shi ne, lokacin da suke ɗaukar ba su san yadda ake sarrafa kyamarar ba da sauran su kamar shi kansa labarin da kuma tace finafinan tare da sarrafa hotunan da yadda ake ɗaukar sa cikin nagarta da inganci da kuma ƙwarewa, don haka muka ga akwai buƙatar su san duk wani abu da zai taimake su wajen inganta sana’ar su.
To a yau shi ne Maigirma Gwamna Abba Kabir Yusif ya sahhale tare da gudunmawar Kwamishinan Yaɗa Labarai Baba Halilu Dantiye aka sahhale domin a zo a ba su wannan horo na kwana biyu, wanda kuma bayan an gama za mu duba mu ga ta ina za mu shigo, don ci gaba da ba su gudunmawa.”
Ya ƙara da cewa ” Ba kurame kawai ba ne a cikin tsari na wannan horo ba, akwai makafi da suke da basira ta waƙa, yadda ta haka ne za mu rinƙa janyo su don su ga cewar wannan abin na kyama yana fita daga cikin zukatan su, kuma suna ganin su ma ‘ya’ya ne za a iya damawa da su a kowacce irin masana’anta.
Don haka muna alfahari da su, kuma muna alfahari da wannan gwamnati ta maigirma zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusif da ta bada dama, a matsayina na ɗan fim Ina so na ga mutane daga sassa daban daban suna sha’awar wannan harkar kuma an zo an tallafa musu ganin cewa harka ce ta matasa wadda an san lokacin da muka fara ta yanzu ga shi har girma ya zo mana, don haka muna yi musu fatan samun nasarori kamar yadda muka samu.
Kuma hakan ya nuna cewa wannan gwamnati ta maigirma zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusif gwamnati ce mai tausayi kuma da take yi da kowa, kuma ta zama abin alfahari ga kowa.
Ina yi wa waɗannan bayin Allah fatan alheri da fatan za su tsaya su nutsu su koyi abin da ake so su koya, yadda za su fito su tallata al’adarmu da addininmu cikin kwanciyar hankali.”
Shi ma a nasa jawabin Gwamnan Kano Abba Kabir Yusif, wanda ya samu wakilcin Kwamishinan yaɗa labarai Baba Halilu Dantiye, ya ce “Saƙon da nake da shi na maigirma zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusif ne, domin shi ne ya bada dama cewa a zo a yi wannan taro na bita wadda take mai abin sha’awa ƙwarai da gaske wadda ba a taɓa yin ta ba, kuma yana daga cikin ɓangare da maigirma Gwamna Abba Kabir Yusif yake nuna kulawa.
Wannan bita da aka shirya wa kurame ta yadda za su iya yin finafinai su ma. Suna da sha’awa amma ka ga saboda yadda yanayin su yake su ma suna da tsarin koyar da su na musamman, saboda haka yanzu an zo za a yi musu wannan bita ta kwana biyu.
Kuma hakan ya samo asali daga shi Shugaban Hukumar tace finafinai da ɗab’i ta Jihar Kano Abba El-Mustapha wanda shi daman harka ce da ya tashi da ita, amma waɗannan mutane ba a shigo da su ba, sai da suka zo suka same shi. Kuma aka ga ya kamata a inganta abin, kuma maigirma gwamna ya amsa tun da suna da sha’awa saboda kowa da akwai baiwar da Allah ya yi masa wadda idan ka ba shi dama sai ka ga ya zama wani abu sosai a ciki, har ya samu ya riƙe kansa da iyalansa, ya kuma tarbiyyantar da wasu.
To wannan shi ne ƙarfin gwiwar da aka bani kuma maigirma gwamna ya amince kuma ya turo ni da na wakilce shi, saboda yanayin aiki ya bani saƙon a yi musu fatan alheri kuma a ƙarfafa musu gwiwa da cewa su riƙe wannan abin sosai tun da yanzu an shigo da su za a yi musu taron bita za a koya musu abubuwa, wanda a baya don kansu suke yi a waya saboda kowa ya iya. Amma kuma ka samu ilimi a kan abin, zai fi inganta maka harkar da kake yi.
To yanzu shi ne aka zo aka fara, wanda in sha Allahu a yanzu farawa aka yi, tun da babu yadda za a yi a cikin kwana ɗaya ko biyu a ce an koyar da dukkan abu amma dai a fara ɗin don kamar makaranta ce, idan ka fara ko da ka gama za ka ci gaba da karance karance don ka ƙara ilimi a kan wanda ka samu, don haka idan aka gama za mu kaiwa maigirma gwamna ya gani ta yadda za a ga ta ina za a ɗora in sha Allah.”
An dai yi taron an gama, kuma da dama cikin kuramen da muka nemi jin ra’ayinsu a kan taron, sun nuna gamsuwar su tare da yaba wa Gwamnan Kano Abba Kabir Yusif bisa kulawar sa da ya nuna a gare su wadda ba su taɓa samun wata gwamnati da ta yi musu hakan ba.
Kuma sun yaba tare da yin godiya ga shugaban Hukumar tace finafinai da ɗab’i ta Jihar Kano Abba El-Mustapha, wanda ya zamo silar kyautatawar da Gwamnatin Jihar Kano ta yi musu.
