Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Dikko Raɗɗa na Jihar Katsina ya ƙaddamar da kwamitin da zai kula da samar da abinci, wanda shiri ne na samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya zai fara a arewa maso yammacin Nigeria.
Shugaban shirin na majalisar ɗinkin duniya wanda ya sami wakilcin Akeem Ajibola, ya bayyana ganin yadda yan bindiga suka ɗaiɗai ta yankin ya sa ƙwarin zai fara shirin raba abincin a yakin.
Ya ƙara da cewa kwamitin zai fi maida hankali akan ‘yan gudun hijira da mata masu juna biyu da mata masu shayarwa waɗanda yan ta’addan suka kashe mazajensu.
Gwamna Raɗɗa kuwa ya yaba da wannan shiri da yac e zai taimaka wa gwamnatin Katsina har ma da gwamnatocin Arewa maso Yamma da ke fama da hare haren ‘yan bindiga.
Ya kuma gode wa Majalisar Ɗinkin Duniya da irin gudunmawar da suke bai wa yankin da zai taimaka wajen farfaɗo da zaman lafiya da bunƙasa tattalin arzikinsu
Kwamitin da gwamnan ya ƙaddamar ya ƙunshin mutum 14 da za su yi aiki ƙarƙashin ofishin mataimakin gwamna.
‘Yan kwamitin sun haɗa da kwamishina cikin gida da tsaro da na harkokin mata da na na aikin noma da sauransu.
