
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Rahotanni daga jihar Zamfara sun bayyana cewa, wani soja ya harbe wani mai suna Halliru Liman wanda DPO ne na ƴan sanda da ke aiki a ofishin Wasagu, a wata matsaya ta bincike.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, ASP Yazid Abubakar ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da jami’in ƴan sandan ke kan hanyarsa ta zuwa Birnin Kebbi a jihar Kebbi don halartar wani taro inda wani soja wanda ɗaya ne daga cikin tawagar atsayen Hadarin Daji ya tare shi a yankin Ɗanmarke da ke ƙaramar hukumar Bukuyum.
Ya ce, an kashe jami’in duk da cewa ya bayyana kansa a matsayin ɗan sanda.
Rundunar ƴan sandan ta buƙaci a zurfafa bincike game da lamarin don tabbatar da kamo waɗanda ke da hannu a ciki tare da hukunta su.
Kazalika, rundunar ta aika da saƙon ta’aziyyarta ga ahalin mamacin tare da yi mu su alƙawarin yin adalci akan haka.
