Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Wani kamfani da ya kware a harkar noman abarba a ranar Litinin ya bayar da shawarar inganta noman kayan marmari, yana mai cewa a kullum ana asarar sama da Naira Miliyan 50 a Nijeriya wajen shigo da abarba daga ƙasashen Ghana da Togo.
Babban jami’in kamfanin na Daɓidorla, Oluwasegun Alabi, a lokacin da yake tattaunawa da ’yan jarida, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da su samar da yanayin da zai samar da haɗin gwiwa don bunƙasa noman abarba a ƙasar.
Ya kuma bayyana cewa kamfanin zai horar da matasan Nijeriya 50,000 aikin noman abarba da nufin mayar da ƙasar kan gaba wajen fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje.
“Don ƙara magance matsalar ƙarancin abinci a Nijeriya, yana da muhimmanci gwamnati ta ƙara shigar da mutanen da suka dace a fannin noma.
“Matsalar samar da abinci a duniya a halin yanzu wata dama ce ta musamman ga Nijeriya a matsayinta na ƙasa bakiɗaya, domin mun mallaki dukkan albarkatun da ake buƙata kamar su kasa mai albarka, yanayi mai kyau, da albarkatun jama’a don zama ƙasar da ta fi kowacce ƙasa samar da abinci a duniya. Don haka, dole ne mu yi aiki a yanzu kuma mu tabbatar da cewa an samar da matakan da suka dace don amfani da wannan damar,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa, duk da ƙaruwar buƙatar abarba a duniya, har yanzu fannin noma a Nijeriya bai yi cikakken amfani da wannan damar ba, ya ƙara da cewa “da yawa daga manoman Nijeriya ba su da ilimin zamani, albarkatun ƙasa, da kayayyakin more rayuwa da ake buƙata domin cika aa’idojin ƙasa da ƙasa.
Da yake ba da misali da alƙaluman Hukumar Abinci da Aikin Noma (FAO), ya ce, “A halin yanzu Nijeriya ce ƙasa ta 8 a yawan noman abarba a duniya inda aka kiyasta adadin ya kai tan 1,607,200 a kowace shekara.”
Ya ƙara da cewa, abin mamaki ne yadda Ghana da jamhuriyar Benin ke noman ƙasa da Nijeriya a duk shekara, amma duk da haka har yanzu Nijeriya na shigo da abarba daga Ghana a matsayi na 13, ita kuma Benin a matsayi na 16 da aka kiyasta adadin ya kai tan 678,079 a duk shekara, da kuma 472,514 bi da bi.
