
Daga BELLO A. BABAJI
Wasu ƴan ta’adda da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun yi fashi tare da ƙone wasu shaguna da gidaje a ƙauyen Mafa da ke ƙaramar hukumar Tarmuwa a jihar Yobe.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, DSP Dungus Abdulkarim ya bayyana hakan a Damaturu, babban birnin jihar, a ranar Litinin inda ya ce kawo yanzu ba su tabbatar da adadin rayukan da aka rasa ba.
Lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 4 na yamma a ranar Lahadi inda wasu mutane biyu daga cikin mazauna yankin suka sanar da rundunar ƴan sandan.
Shaidun sun ce mayaƙan sun shigo ƙauyen ne a sama da babura 50 ɗauke da waɗansu muggan makamai inda suka farmaki mutane tare ƙone shaguna da gidaje.
Mayaƙan sun kuma bar waɗansu takardu da ke ɗauke da rubutun Arabiyya.
