
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba ya sassaci game da ƙalubalen da ake fuskanta a lamuran tsaro a Nijeriya.
Shettima ya faɗi haka ne a lokacin da ya karɓi baƙoncin shugabannin gidan labarai na News Agency Nigeria (NAN) a Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Ya ce, akwai buƙatar haɗin-gwiwa na shiyyoyi da kuma al’ummar yankunan don warware matsalolin da taɓarɓarewar tsaro ta haifar a yankin Afirka ta Yamma.
Ya kuma yi nuni da yadda hakan yayi tasiri a Nijeriya da ƙasashen da take maƙoftaka da su inda gidajen jaridu na da muhimmanci wajen kawo ƙarshen matsalolin da ke addabar al’umma.
Haka nan, Mataimakin shugaban ƙasar yayi tsokaci game da taron da NAN ta shirya na harkar jarida musamman don rawar da ta ke takawa wajen shawo kan matsalolin taɓarɓarewar tsaro a Nijeriya da wasu yankunan.
