Hukumar ƙwallon Kwando ta Duniya (FIBA) ta bayyana cewa, ƙungiyar ƙwallon ƙwando ta Mata ta Nijeriya, D’Tigress, ta hau matsayi na takwas a jerin ƙasashe na duniya bayan rawar da ta taka a Gasar wasannin Olympics na 2024 a Paris.
A ranar Alhamis FIBA ta fitar da jerin sunayen ƙasashen.
Wannan ƙarin matsayi ya tabbatar da matsayinsu a cikin manyan ƙungiyoyi goma na duniya, wanda ya sa suka zama ƙungiyar Afirka ta farko, maza ko mata, da ta kai wannan matsayi a jerin ƙasashe na duniya na FIBA.
ƙungiyar ta D’Tigress, it ace ta farko a nahiyar Afirka da ta taɓa kai wa zagayen wasan kusa da na ƙarshe a wasannin na Olympics.
