Gwamnatin Katsina za ta kafa kwamitin ci gaban al’umma

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin jihar Katsina za ta kafa kwamitin ci gaban al’umma a kowacce ƙaramar hukumar da ke jihar.

Gwamna Dikko Raɗɗa ya sanar da haka a wajen taron tattaunawa da alummomin shiyyar Katsina ya ce, nan bada jimawa ba za a aika da ƙudirin wa majalisar dokoki ta jihar domin ta amince ya zama doka.

Ya ce, manufar kafa wannan kwamiti shine bai wa al’umma dama su yanke wa kansu abinda suke buƙata gwamnati ta yi masu.

Haka kuma, kwamitin zai sa ido akan aikace-aikace na gwamnatin jihar a yankunansu domin tabbatar da ingancin aikin.

Malam Dikko Raɗɗa ya ƙara da cewa kwamitin zai sa ido akan harkan tsaro a yankunan nasu domin su suka san kowa da zarar baƙon ido ya shigo su sanar da jami’an tsaro.

Ya ƙara da cewa, bayan wannan kwamiti da shi zai jagoranta akwai ƙananan kwamitoci da za a kafa da za su yi aiki kafaɗa-da-kafaɗa da babban kwamiti.

Duk kwamitocin za su yi aiki tare da ƙananan hukumominsu domin samun nasarar ƙudirin gwamnatin na tabbatar da adalci wajen raba arziƙin jihar da gudanar da ayyukan raya ƙasa a sassan jihar.

Gwamnan ya kuma sanar da cewa kwamitin zai ƙunshi mutane 20 a kowace ƙaramar hukuma da suka haɗa da limamai, mai gari, matasa, mata, manoma da kansilar yankin.

Haka kuma, gwamnan ya bayyana cewa gwamnati za ta tanadi ofis a kowacce ƙaramar hukuma da ma’aikata da za a ɗakko daga ƙananan hukumomin da suke, tare da samar masu da kayan aiki.

Gwamnatin ne ta shirya taron tattaunawa da jama’a domin jin koke-kokensu da buƙatar su akan kasafin ƙudin 2025.

Gwamnan ya riga ya kammala ziyarar shiyyar guda uku; Funtua, Daura da Katsina.

Ya tabbatar wa al’ummar cewa ya saurari ƙorafe-ƙorafensu sai dai gwamnati ba za ta iya biyan duka buƙatunsu ba amma za ta yi abinda zata iya yi .

Malam Dikko Radda ya kuma yi kira ga jama’a su tashi tsaye wajen kera kawunansu.

By Babaji