Na fito takarar shugabancin ƙaramar Hukumar Dutse ne don kyautata cigaban al’umma – Hon Siba

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

ɗan takarar shugaban ƙaramar hukumar Dutse ta Jihar Jigawa a ƙarƙashin Inuwar jam’iyyar APC, Dakta Siba Abdullahi ya bayyana cewa kiran da al’ummar Dutse suka yi masa na ya shiga takarar ce tasa ya fito ba domin ra’ayin kansa ba.

Ya bayyana haka ne da yake zantawa da ‘yan jarida ya ce da yardar Allah idan ya yi nasara zai yi ƙoƙari wajen assasa cigaban ilimi da lafiya da gudanar da ayyuka da bunƙasa walwalar jama’a zai kuma tabbatar da gudanar da waɗannan ajandodi guda huɗu domin cigaban yankin.

Ya ƙara da cewa yanzu haka takarar tasa ta samu mutuƙar karɓuwa ba kawai a jam’iyyarsu ta APC ba hatta sauran jam’yyyu suna ba shi goyon baya domin sun amince da ingancinsa.

Sannan sai ya yi kira ga al’ummar ƙaramar hukumar Dutse su cigaba da ba shi haɗin kai da hoton baya lokacin zaɓe su zaɓi jam’iyyar APC su kai nasara da za su gudanar da ayyuka ga cigaban al’umma.

Hon. Dakta Siba Abdullahi ya nuna mutuƙar godiya ga al’ummar ƙaramar hukumar Dutse musamman matasa maza da mata da dattawa da jagororin su na siyasa bisa irin goyon baya  da addu’o’i na kaiwa ga nasara da suke masa da yardar Allah nasarar sa za ta zama alkhairi ga cigabanta ƙaramar hukumar Dutse.

By ukarofi