Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe
An bayyana shirin ‘Adolescent Girls Initiatiɓe for Learning and Empowerment’ (AGILE) a matsayin wani shiri da zai iya magance matsalolin da suka shafi ilimin ’yan mata nan gaba kaɗan.
Kwamishinan Tsare-tsare da Tattalin Arziki na Jihar Gombe ne Alhaji Salihu Baba Alkali, ya bayyana haka a yayin da ya karɓi tawagar shirin AGILE, waɗanda suka kai ziyara ta wayar da kai a ofishinsa.
Alhaji Salihu Baba Alkali ya yaba wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya bisa amincewa da shigar jihar cikin shirin, tare da bayyana cewa ma’aikatarsa za ta ɗauki matakan da suka dace domin tabbatar da aiwatar da shirin cikin tsari a jihar.
Tun da farko, Ko’odinetan Shirin, Dakta Amina Haruna Abdul, ta bayyana cewa ziyarar na ci gaba da wayar da kan ma’aikatun gwamnati ne kan shirin. Ta tabbatar wa kwamishinan cewa za su yi aiki tare da ma’aikatar don samun nasarar shirin a jihar.
Dakta Amina ta bayyana manufofin shirin tare da tabbatar da cewa tawagar za ta yi aiki tuƙuru don amfanin dukkan al’ummomin jihar. Haka kuma, ta yi nuni da cewa shirin yana da ma’anar haɗa dukkanin masu ruwa da tsaki a cikin dabarun aiwatarwa a Jihar Gombe.
